Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 19:47:37    
Kungiyar wasan hoki a fili ta mata ta Argentina ta lashi takobin kwashe lambar zinariya a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Ana kyautata zaton cewa, kungiyar wasan hoki a fili ta mata ta kasar Argentina za ta iso nan birnin Beijing a ranar 28 ga watan da muke ciki don halartar gasar wasannin Olympics ta 29 ta Beijing. A matsayin wata zakarar wasan hoki a fili a duniya, kungiyar wasan hoki ta mata ta kasar Argentina ta lashi takobin kwashe lambar zinariya a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Wakiliyarmu ta samu damar daukar labari kan yadda kungiyar wasan hoki ta mata ta Argentina take samun horo a wani filin wasan kwallon hoki dake filin birnin Auenos Aires, babban birnin kasar, inda ta ga 'yan wasan suna himmantuwa wajen samun kyakkyawan horo ko da yake akwai dan sanyi kadan a lokacin.

Wata 'yar wasa mai suna Alejandra Palma ta fada wa wakiliyarmu cewa, hasali ma, kungiyarmu ta soma share fagen halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing ne jim kadan bayan da aka kawo karshen gasar wasannin Olympics ta Aden a kasar Girka. Kuma kungiyarmu ta taba samun lambar azurfa da kuma lambar tagulla a cikin wasannin Olympics da aka gudanar a shekarar 2000 da kuma shekarar 2004. Abun bakin ciki shi ne ba mu taba samun lambar zinariya a fannin irin wannan wasa ba. Miss. Palma ta furta cewa: " Ko shakka babu, masu koyar da mu, da malamai masu bada jagoranci ga samun fahohi da kuma dukkan 'yan wasan kungiyarmu sun bayyana aniyar samun lambar zinariya a gun gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Beijing na kasar Sin."

Ko da yake kungiyar Argentina tana da babban karfi a fannin wasan hoki a fali, amma duk da haka, a idon 'yar wasa Palma, kungiyar kasarta da wassu kakarfan kungiyoyi na duniya suna kan matsayi kusan daya. Saboda haka ne, ta ce wajibi ne su kara kokari wajen samun horo. Tana mai cewa :' A ganina, manyan abokan karawarmu sun haka da kungiyar kasar Holland wadda take kan gaba a duniya, da kungiyar kasar Jamus da kuma kungiya kasar Australiya. Babu tantama akwai kungiyar kasar Sin wadda ta samu ci gaban a-zo-a-gani a 'yan shekarun baya.'

Daga baya dai, 'yar wasa Palma ta bayyana cewa, da yake kungiyar wasan hoki ta mata ta kasar Argentina ta taba zuwa kasar Sin a watan Yuli da watan Agusta na shekarar bara, shi ya sa ta saba da muhallin gasa. A lokaci guda, ta buga babban take ga ayyukan share fagen gasar wasannin Olympics ta Beijing. Tana mai cewa: "Lallai filaye da dakunan wasannin Olympics sun kasance abun mamaki. Tuni a shekarar bara, an kammala gina filin wasan kwallon hoki, wanda ya burge mu kwarai da gaske!"

A shekarar bana, a karo na biyu ne 'yar wasa Palma da sauran abokanta za su zo nan Beijing. Ta yi farin ciki matuka da fadin cewa : "Lallai kasar Sin ta ba ni kyakkyawar alama a cikin zuciyata. Muna masu sha'awar al'adu da kuma tarihi na kasar Sin. A lokacin, mun samu damar yin yawon bude ido a Babbar Ganuwar Sin, da Filin Tian An Men, da Gidan sarakuna da kuma lambun shan iska na Yi He Yuan da dai sauran ni'imtattun wuraren tarihi".

To, madalla jama'a masu sauraronmu, kun dai saurari sabon shirinmu na " Daukar labarai kan kungiyoyin 'yan wasa a gasar wasannin Olympics ta Beijing". Ni Sani Wang ne ya fassara wannan shiri kuma ya karanto muku shi. A madadin kowa da kowa na Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin ne nake cewa sai makon gobe war haka, in Allah ya kai mu. (Sani Wang)