Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 16:33:00    
Waiwaye adon tafiya(5)

cri

Lubabatu: Masu sauraro, a nan sashen Hausa, ban da ma'aikata Sinawa, akwai kuma wasu ma'aikatan da suka zo daga kasashen Nijeriya ko Nijer, kamar malam Amada Bacha da ya zo nan sashen Hausa a lokacin farkon kafuwarsa da malam Hamidu wanda ya dade yana aiki a nan sashen Hausa har tsawon shekaru 19 da dai sauransu, wadanda suka ba da taimako kwarai da gaske ga cigaban sashen Hausa. Yau ga shi na gayyaci wasu ma'aikatan sashen Hausa biyu da suka zo daga Nijeriya?kuma ina tsammanin ta muryarsu ne za ku iya gane su wane ne, amma duk da haka, da farko dai, bari su gabatar da kansu zuwa gare ku.

Lawal:To, masu sauraro, assalamu alaikum, barkanmu da war haka, kamar yadda aka sani dai, ni ne Lawal Mamuda, kuma ina muku marhabin da saduwa da ku a cikin wannan shiri na musamman wanda Lubabatu ta shirya.

Balarabe:To, masu sauraronmu, a daidai wannan lokaci, assalamu alaikum, barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shiri namu na musamman, kuma sunana Balarabe Shehu Ilelah.

Lubabatu:To, shin yaushe ne kuka fara aiki a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin?

Lawal:To, zan so abokin aikina Balarabe Shehu Ilelah ya soma gabatar da kanshi ko shekaru nawa yana aiki a nan sashen Hausa, sabo da idan aka kwatanta ni da tsohon ma'aikacinku Balarabe Shehu Ilelah, Bismillah.

Balarabe(dariya):To, masu sauraro, sunana kamar yadda na fada muku Balarabe Shehu Ilelah, ni mutumin Bauchi ne, kuma na soma aikin jarida a nan telebijin na Bauchi. Na fara aiki a nan sashen Hausa tun wajen shekarar 1991, wato yau shekaru nawa ke nan, kin fi ni yin lissafi?

Lubabatu:17?

Balarabe: Kusan shekaru na 17, tun lokacin da na zo nan din, shekaru 17 na yi aiki a nan gidan rediyo, amma ba duka ba, domin na dan katse, na yi aiki a jami'a, inda na koyar a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, kuma har ga shi yanzu ina nan ina aiki a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Lawal:To, na zo dai daga Nijeriya, kuma ina aiki a Voice Of Nigeria, wato muryar Nijeriya, to, daga can ne Allah ya kawo ni nan wurin, na zo aiki a nan sashen Hausa na rediyon CRI, kuma yau ga shi Allah ya kawo mu har na cika shekaru biyu ke nan ina aiki a nan sashen Hausa na rediyon CRI.

Lubabatu:To, kafin zuwanku nan sashen Hausa, ko kun taba kasancewa masu sauraron sashen Hausa na rediyon kasar Sin?

Bala: To, mu kan saurari sashen Hausa na rediyon kasar Sin, tun da mu 'yan jarida ne, kuma duk dan jarida idan har shi dan jarida ne, ya kan yi sha'awar sauraron gidajen rediyo da dama, domin me? Domin sanin me ake ciki a wadannan kasashe. To, a gaskiya, sashen Hausa na rediyon kasar Sin na daya daga cikin tashoshin da ni dai ina matukar sha'awar saurara a lokacin, mutane su kan yi mamaki su ji Sinawa suna Hausa, kuma wannan ma kadai ya kan ba duk wani Bahaushe alfahari, ko farin cikin jin cewa, ga wancan, kamar yadda muka dauka a Nijeriya, ake cewa, "Sin bangon duniya", har ga wani a can bangon duniya, yana iya yin harshen Hausa, ba ma kawai yana magana da harshen Hausa ba, a'a, har ma ga shi yana watsa labaru da sashen Hausa. To, a lokacin ne muka samu mutane kamar su Halima, su Ali, su malam Musa, da dai sauransu. Har sai ga shi a lokacin, muke ta tunani, to ga wannan kasa mai nisa, ko wata rana Ubangiji Allah zai sa ni ma in je wannan kasa, ko ma da yawo. Sai ga shi wani bangare na rayuwata, lokacin da nake cikin karfina, kusan ma duk a nan kasar Sin ne, kin ga wannan wani abu ne, wanda ke nan mafarki ya zama gaskiya, wato abin da kake tunani a da kamar ba zai yiwu ba, sai ya yiwu yanzu. Kin ga wannan wani abu ne abin alfahari kwarai da gaske a gare ni.

Lawal:Na fara sauraron wannan gidan rediyo ne tun yana gidan rediyon Peking, tsohon suna na rediyon kasar Sin ke nan. A lokacin, ba ma sauraron rediyo muka abin ba, ta wasiku da 'yan hotunan da suka aika wa masu sauraro, akwai su da kokarin aikawa da hotuna, suna aiko mana da wasiku, muna ganin hotuna, to, tun daga lokacin ne na fara sanin rediyon kasar Sin.

Lubabatu:A tsawon lokacin da kuke aiki a sashen Hausa na rediyon kasar Sin, musamman ma Balarabe, ma iya cewa, ka gane ma idonka bunkasuwar sashen Hausa, to, ko za ka iya tunawa da yaya sashen Hausa yake a lokacin farkon zuwanka?

Bala:To, wannan ita ce babbar tambaya, wadda zan iya wuni guda ina ba ki amsa, Da na zo sashen Hausa, a lokacin, sashen Hausa ba inda muke ba ne yanzu, a lokacin, yana wani babban titin da ake kira Fuxinmen, a wani ginin da ake kira Guangbo Dalou.

Lubabatu:Guangbo Dalou?

Balarabe:E, watakila kin san wannan gini din?

Lawal:Ko ta ji ana fadi.

Bala: To, kin ga da na fara aiki da sashen Hausa na rediyon kasar sin, lokacin, tsohon gini ne, muna hade da ma'aikatar farfaganda ko watsa labarai, duk a wuri guda. A lokacin, muna amfani ne da irin tsohon faifan nan wanda ake nadewa, idan za mu yi labaru, sai a dauko, wani lokaci mu yanke, a murza da hannu.

Lubabatu:Ba kamar yanzu da muke amfani da inji mai kwakwalwa ba?

Bala:A'a, ba kamar yanzu ba, yanzu an ci gaba sosai. Sa'an nan, a lokacin, ba computer, kawai muna labarai ne da keken rubuta. Daga baya, muka kaura daga can, muka dawo sabon gini, inda muke ke nan a yanzu. Kuma idan kin dauki labaranmu na da da na yanzu, za ki ga akwai bambanci ga shirye-shiryenmu, yanzu akwai "cigaban kasar Sin", "Sin da Afirka", "me ka sani", akwai "kiwon lafiya", yanzu muna tabo kowane sashe na zaman rayuwa, sabo da haka, muna tafiya daidai da cigaban kasar Sin, muna shiga harkokin tattalin arziki, muna shiga harkokin siyasa da zaman takewa, kowane bangare yanzu muna da shirye-shirye a kansa, wannan ba karamin cigaba ba ne aka samu.

Lubabatu:To, a tsawon lokacin da kuke sashen Hausa, ko akwai abubuwan da suka burge ku, har watakila ba za ku iya mantawa da su ba har abada?

Lawal:Abubuwan da suka burge mutum a nan sashen Hausa, ni ina ji kullum cigaba suna burge ni, da kuma ba ni al'ajabi, domin yau a ce, Basini shi ne zai yi Hausa, kuma Bahaushe ya gane. Abin burgewa ne.

Bala:Sa'an nan kuma, wani abu guda, a tsawon aikin da dukanmu muka yi, na san abokin aikina shi ma haka ne, babban abu shi ne zaman tare da abokan aikinmu Sinawa, a zauna lafiya, a yi wasa da dariya, a yi aiki, a taimaki juna, wata rana za ka bar wurin, kuma za ka bar abin da Turawa ke cewa "memory", wato a bar baya mai kyau, ka bar tunani mai kyau, to, duk wadannan ba za mu iya mantawa da su ba har iya tsawon rayuwarmu.

Lawal:Akwai wani abu kuma, ka ga al'adun Sinawa suna da ban sha'awa, sabo da idan wata hidima ta same ka, ka ga sun yiwo kungiya, domin ka ga a lokacin Nuwamba da aka yi suna a gidana, sun yiwo kungiya sun zo gidana sun taya ni bikin suna. Ka ga wannan zumunci ne, suna da zumunci kwarai da gaske.

Lubabatu:To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na "waiwaye adon tafiya", tare da fatan kun ji dadin shirin, kuma da haka, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, ku kasance lafiya.(Lubabatu)