Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 21:24:58    
Jihar Tibet ta ci gajiya ga babbar moriyar jama'a kai tsaye

cri

A 'yan kwanakin baya, shugaban jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin Mr. Qiangba Puncog ya bayyana cewa, har kullum jihar Tibet tana mai da hankali sosai kan zaman rayuwar jama'ar jihar, ta ci gajiya ga babbar moriyar jama'a kai tsaye.

A kan gidajen kwana, ya zuwa shekarar 2007, manoma da makiyayya da yawansu ya zarce dubu 570 na jihar Tibet sun samu gidajen kwana masu kyau.

A kan kiwon lafiya, dukkan manoma da makiyayya na jihar Tibet suna da inshorar likilanci bisa tushen ganin likita ba tare da biyan kudi ba.

Jihar Tibet tana mai da hankali sosai kan jama'ar da ke fama da matsaloli a zaman rayuwarsu. A shekarar 2007, an shigar da dukkan manoma da makiyayyai da ke fama da talauci cikin tsarin tabbatar da mafi karancin jin dadin rayuwar jama'a, wadanda yawansu ya kai dubu 230. Game da tasirin da lamuran tashe tashen hankula da suka faru a ranar 14 ga watan Maris a birnin Lhasa da kuma karuwar farashin kayayyaki, gwamnatin jihar Tibet ta yanke shawarar kara ba da rangwamen kudi ga dukkan jama'ar da ke cikin tsarin tabbatar da mafi karancin jin dadin rayuwar jama'a a ko wane wata.(Danladi)