Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 17:21:18    
Wata kyakkyawar ziyarar zurfafa hulda a tsakanin Sin da Japan

cri
A lokacin da furanni ke tohowa, wato a ran 6 ga wata, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai fara yin ziyarar aiki a kasar Japan. Wannan ziyarar aiki ce da shugaban kasar Sin zai sake yi a kasar Japan bayan shekaru 10 da suka wuce. Ziyarar kuma za ta zama wata kyakkyawar ziyarar da shugaban kasar Sin zai yi a kasar Japan don inganta hulda a tsakanin Sin da Japan.

Malam Ma Junwei, mataimakin shugaban sashen nazarin harkokin Japan na cibiyar nazarin huldar zamanin yanzu ta kasa da kasa ta Sin yana ganin cewa, a cikin sama da shekara daya da ta wuce, bisa kokarin da shugabannin kasar Sin da ta Japan suka yi, an yi ta kyautata hulda a tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, "bayan da Abe Shinzo ya maye gurbin Junichiro Koizumi ya zama firayim ministan kasar Japan a shekarar 2006, da farko ya zabi ziyarar kasar Sin, ta haka dai ne manyan shugabannin kasar Sin da Japan sun sake fara yi wa juna ziyara, bayan da suka daina yinta a cikin shekaru 6 da suka wuce. Bayan misalin rabin shekarar da Abe Shinzo, firayim ministan kasar Japan ya kawo wa kasar Sin ziyara, sai Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin shi ma ya kai ziyara a kasar Japan. Ta ziyarar, an kara daidaita batutuwa da yawa da ke kasancewa ga hulda a tsakanin Sin da Japan. Kazalika bayan da Mr Fukuda Yasuo ya zama sabon firayim ministan kasar Japan, yana kara dora muhimmanci ga huldar kasashen biyu har fiye da Abe Shinzo."

Ta haka ana ci gaba da yalwata hulda a tsakanin Sin da Japan bisa takardun siyasa uku wato "sanarwar hadin gwiwar Sin da Japan" da "yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta a tsakanin Sin da Japan" da kuma hadaddiyar sanarwa a tsakanin Sin da Japan. Malam Liu Jiangyong, masanin huldar kasa da kasa ta Jami'ar Qinghua ya bayyana cewa, a sakamakon kara inganta hulda a tsakanin Sin da Japan, ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a wannan gami za ta sabunta hulda a tsakanin kasashen biyu. Ya ce, "wadannan takardun siyasa uku tushen siyasa ne ga huldar da ke tsakanin Sin da Japan. Musamman ma shekarar nan zagayowar shekara ta 30 da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da sada zumunta a tsakanin kasar Sin da Japan, amma za a sabunta wasu abubuwa da ke cikin wadannan takardun siyasa uku bisa yalwatuwar halin da ake ciki a kasashen biyu da kuma yalwatuwar halin da ake ciki a duniya. A shekarar 1998, kasashen biyu sun kulla huldar abokantaka ta hadin gwiwa da aminci don tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa, a kwanakin baya, sun sami ra'ayi daya a kan huldar da za su kulla don moriyar juna bisa manyan tsare-tsare, a ganina, mai yiwuwa ne, ta ziyarar shugaba Hu Jintao, za a gabatar da wasu sabbin ra'ayoyi don kara inganta hulda a tsakanin kasashen biyu."

Abubuwan da suka faru a cikin shekaru da yawa da suka wuce, sun shaida cewa, idan kasar Sin da Japan sun yi zaman jituwa a tsakaninsu, za su sami fa'ida tare, bamban da haka idan kasashen biyu ba su yi zaman jituwa a tsakaninsu ba, to, za su sha hasara tare. Da zuciya daya, jama'ar kasashen biyu suna fatan ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a kasar Japan za ta kara inganta hulda a tsakanin kasashen biyu. Malam Ma Junwei yana ganin cewa, "yanzu Sin da Japan manyan kasashe biyu ne a nahiyar Asiya kuma a iya cewa haka a duniya. Sabo da haka halin da ake ciki game da hulda a tsakaninsu ya iya kawo tasiri ga halin da ake ciki a Asiya da duniya a wasu fannoni. Tabbas ne, ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi a kasar Japan a wannan gami za ta sa kaimi ga yalwata hulda a tsakanin kasashen biyu, kuma za ta sa hulda a tsakanin kasashen biyu da ta kawo kyakkyawan tasiri ga halin da ake ciki game da zaman lafiyar Asiya da ta duniya." (Halilu)