Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 16:57:47    
Wasu mutame masu ilmi na kasashen Turai sun fallasa asalin "aikace-aikacen neman 'yancin Tibet"

cri

A kwanakin baya, bi da bi ne wasu mutane masu ilmi na kasashen Turai suka rubuta bayanai domin fallasa asalin "aikace-aikacen neman 'yancin Tibet".

Mr. Michel Chossudovsky direkatan cibiyar nazarin hadaddiyar duniya ta kasar Canada kuma marubucin "Encyclopedia Britannica" ya bayar da labari cewa, al'amarin ta da manyan laifuffukan da aka yi a Tibet "wani al'amari ne da aka shirya". Sabo da wasu shugabannin kasashen Turai sun zargi kasar Sin, nan da nan kafofin watsa labaru suka fara yada jita-jita kan kasar Sin.

Mr. F. William Engdahl mai ilmi kan fannin tattalin arziki da siyasa na kasar Amurka ya rubuta cewa, mummunan tashin hankalin da ya faru a Tibet shi ne wani mummunan aikin da kasar Amurka ta taka rawa domin lalata zaman karko na kasar Sin.

Mr. Juergen Rose Laftanar Kanar sojojin kasar Jumus ya bayar da labarin jarida kan "Unsere Zeit", inda ya ce, kasashen yammacin duniya suna da hannu kan batun Tibet.