Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 16:12:16    
Jama'ar kasar Japan suna sa ran alheri ga ziyarar shugaba Hu Jintao

cri
A ran 4 ga wata da dare, shugaban kwamitin sada zumunta tsakanin kasar Japan da kasar Sin Mr. Muraoka Kyuhei ya bayyana a birnin Tokyo cewa, jama'ar kasar Japan suna sa ran alheri ga ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai yi wa kasar Japan ba da dadewa ba, kuma yana fatan ganawar dake tsakanin manyan shugabanin kasashen biyu za ta iya sa kaimi ga ci gaban dangantaka mai zaman karko dake tsakanin bangarorin biyu.

A gun liyafar maraba da zuwan tawagar wakilan samarin kasar Sin dake kai birnin Tokyo a ran nan don yin ziyarar sada zumunta a kasar Japan, Mr. Muraoka Kyuhei ya ba da jawabi cewa, ko da yake wa'adin ziyarar tawagar gajere ne, amma yana fatan membobin tawagar za su iya yin amfani da ziyarar nan, su kara fahimtarsu game da al'adar jama'ar kasar Japan, haka kuma su kawo zumuncin da jama'ar kasar Japan suka yi wa kasar Sin cikin sahihanci.

Shugaban tawagar kasar Sin kuma sakatare na sakatariyar kwamitin tsakiya na kungiyar matasa ta kwaminis ta Sin madam Zhang Xiaolan ta yi godewa ga bangaren Japan sabo da shirye-shiryen da suka yi. Ta bayyana cewa, matasa suna da nauyin raya kasashen biyu a kan wuyansu, ya kamata su yi kokari tare wajen sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Japan cikin lami lafiya bisa matsayin dogon lokaci da hangen nesa. (Zubairu)