Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 15:31:20    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya a babban filin ciyayi da ke gabashin garin Wuming na jihar Guangxi ta kasar Sin, an buga ganguna don fara bikin rera wakoki na "ran 3 ga Maris" na gundumar Wuming wato garin kabilar Zhuang na kasar Sin, 'yan kabilar Zhuang fiye da dubu 10 da bakin da suka zo daga sauran wurare masu nisa sun tada murya sama suna rera wakoki domin murnar wannan gagarumin biki.

Kabilar Zhuang wata kabila ce wadda ta fi yawan mutane daga cikin kananan kabilun kasar Sin, wato yawan mutanenta ya kai fiye da miliyan 19, daga cikin su kuma da akwai mutane fiye da miliyan 16 wadanda suke zama a jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta. Jama'ar kabilar Zhuang sun kware wajen rera wakoki, rera wakokin tudu da saurarar wakoki da kuma bikin rera wakoki duk wadannan ayyuka sun zama babban taken zamar rayuwar 'yan kabilar Zhuang wanda ba zai canja ba har abada.

Ran 3 ga Maris ranar bikin gargajiya ce ta kabilar Zhuang, Muhimmin aikin da aka yi a gun wannan biki shi ne rera wakoki, sabo da haka akan kira wannan biki da sunan "bikin waka". A gun bikin akan rera wakoki tsakanin mutane 2 ko mutane da yawa ta hanyar yin tambaya da ba da amsa. Muhimman abubuwan da suka rera cikin wakokin su ne, soyayya da aikin kawo albarka da yanayi da tarihi. Bisa ci gaban da aka samu wajen zaman yau da kullum, akan kara wasu sabbin abubuwan zamani a cikin wakokin da aka rera.

---- Daga ran 8 ga wata, a hukunce ne aka fara sayar da manhaja kan "Albarkatun koyar da harshen Mongoliya" na rukuni na farko na jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin.

Muhimman ma'aikata masu kaddamar da wannan manhaja sun bayyana cewa, wannan rukunin "Albarkatun koyar da harshen Mongoliya" yana hade da fannonin ilmi guda 10 ciki har da harshe da yin lissafi wato mathematics, da yanayin halittu wato physics, da sannin kananan halittu wato biology da sanin dokokin magunguna wato chemistry, amma dukkansu na harshen Mongoliya ne domin 'yan makarantun firamare.

Aikin sayar da "Albarkatun koyar da harshen Mongoliya" a hukunce zai kyautata fasahar ba da darussa ga 'yan makarntu da harshen Mongoliya ta hanyar internet, kuma zai inganta aikin ba da ilmi da harshen Mongoliya.(Umaru)