Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 15:18:00    
Za a gina gidan baje kolin kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na kudu maso gabashin Tibet a yankin Linzhi na jihar Tibet

cri
Lardin Fujian na kasar Sin da ke ba da taimako ga yankin Linzhi na Tibet zai kara ware kudaden musamman da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 5 ga yankin Linzhi na Tibet don mayar da wani ginin da aka kira Niyangge kuma ke da alamar yankin Linzhi a taswira don ya zama wani gidan baje kolin kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na kudu maso gabashin Tibet don ci gaba da haka kayayyakin tarihi da kare su da kuma bayyana su a wuri gu daya.

Yankin Linzhi da ke kudu maso gabashin Tibet, yanki ne mai ni'ima tare da wadata sosai, yana da wuraren yawon shakatawa da yawa da ke da halayen musamman, kabilar Tibet da Han da Menba da Lhoba da Hui da Nu da Drung da Lisu da sauran kabilu suna zaman rayuwa daga zuri'a zuwa zuri'a. Muhallin da yake ciki da abubuwan da yawa da ya samu a tarihi tare da kabilu da yawa da suke zama a cunkushe sun sa yankin Linzhi da ya sami abubuwan tarihi na al'adu da yawa tare da al'adar gargajiya mai wadata da halayen musamman .

Ginin da ake kira sunansa da cewar Niyangge da ke garin 8.1, hedkwatar yankin Linzhi shi ne gini irin na salon Tibet da ke da halayen musamman na al'adun Tibet. Sassan yawon shakatawa da al'adu na Tibet sun bayyana cewa, za a mayar da ginin "Niyangge" don ya zama gidan baje kolin da ke da babban batu, ba ma kawai za a iya kara halayen musamman na al'adun Tibet ba, hatta ma za a iya ci gaba da yada kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba na kudu maso gabashin Tibet da al'adun kabilun da yankin Linzhi shi kadai ya samu da kuma sa kaimi ga raya sha'anin yawon shakatawa, aikin na da ma'ana sosai.(Halima)