Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 14:25:58    
An kusan tabbatar da makasudin samun ilmi tilas a shiyyoyin kabilar Tibet da ke lardin Sichuan na kasar Sin

cri
Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an samun manya sauye- sauye a shiyyoyin kabilar Tibet da ke lardin sichuan na kasar Sin wajen sharudan kafa makarantu da kuma halayen tafiyar da harkokinsu, sabo da haka an samu nasara a shiyyoyin da 'yan kabilar Tibet ke zama wajen aikin kusan tabbatar da makasudin samun ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 da yaki da jahilci ga samari da manya.

A shekarar 2000, gwamnatin lardin Sichuan ta fara gudanar da "shirin shekaru 10 na bunkasa aikin ba da ilmi ga shiyyoyin kabilar Tibet da ke wannan lardi", shirin ya tsai da cewa, cikin shekaru 10 masu zuwa, za a ware kudin Sin Yuan miliyan 300 a kowace shekara domin ba da taimako ga aikin kusan tabbatar da makasudin samun ilmi tilas na makarantu masu tsarin karatu na shekaru 9 da yaki da jahilci ga samari da manya a shiyyoyin da 'yan kananan kabilu ke zama.

A shekarar 2001, lardin Sichuan ya tsai da cewa, birnin Chengdu da sauran shiyyoyi masu ci gaba na lardin za su ba da taimako ga makarantun gundumomi da ke shiyyoyin kananan kabilu. Cikin shekaru 7 da suka wuce, an aika da malaman koyarwa fiye da 3750 zuwa shiyyoyin kabilar Tibet domin ba da taimako ga aikin ba da ilmi, da ware kudin taimako fiye da Yuan miliyan 44 ba tare da neman biyan kamasho ba ga wadannan shiyyoyi. (Umaru) 080505