Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 11:12:34    
Kabilun Tibet daban-daban ba su samu zaman jin-dadi cikin sauki ba, ya kamata a kara darajanta shi, a cewar Erdeni Qoigyi Gyibo

cri
Yayin da Erdeni Qoigyi Gyibo, Panchen na 11  ke halartar gagarumin bikin nune-nune na "Tibet ta da da ta yanzu" a fadar al'adun kabilu ta Beijing jiya 4 ga wata, ya bayyana cewar, kabilun Tibet daban-daban ba su samu zaman jin-dadi cikin sauki ba, shi ya sa kamata ya yi a kara darajanta shi.

A gun taron, kayayyaki 160 da hotuna sama da 400 sun sake shaida cewar, ko a da ko a yanzu, Tibet wani yanki ne da ba za'a iya raba shi ba daga kasar Sin. Wadannan abubuwa sun nuna bunkasuwar Tibet bayan da ta samu 'yancin kanta cikin ruwan sanyi a shekarar 1951, wato daga zaman kangin talauci zuwa zaman wadata, daga mulkin kama-karya zuwa mulkin dimokuradiyya, daga rufe kofa zuwa bude kofa ga kasashen ketare.

Bayan ziyararsa, Panchen na 11 ya ce, hakikanan abubuwa sun shaida cewar, Tibet ta sami bunkasuwa kwarai da gaske ne a sanadin kulawar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin cikin sahihanci, da cikakken goyon-baya daga mutanen duk kasa, da matukar kokarin da al'ummomin Tibet suka yi kafada da kafada. A matsayin wani dan fagen addinai, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan kishin kasar Sin da kishin addini, da bin dokoki da ka'idoji, da bayar da gudummowa wajen tabbatar da zaman jituwa da kwanciyar hankali da zaman wadata na Tibet, da dinkuwar duk kasar Sin gaba daya.(Murtala)