Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 10:51:55    
Jami'an gwamnatin tsakiya ta kasar Sin sun tuntub wakilan Dalai lama

cri

Bisa bukatu sau da dama da bangaren Dalai lama ya yi, a ran 4 ga wata a birnin Shenzhen da ke kudancin kasar Sin, Mr. Zhu Weiqun da Mr. Sitar jami'ai na hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin tsakiya ta kasar Sin sun tuntuba da Mr. Lodi Gyari da Mr. Kelsang Gyaltsen wakilan Dalai lama.

Mr. Zhu Weiqun da Mr. Sitar sun yi nuni da cewa, kullum gwamnatin tsakiya tana aiwatar da manufa iri daya ga Dalai lama a zahiri, tana bude kofa ga Dalai lama wajen yin shawarwari.

Mr. Lodi Gyari da Mr. Kelsang Gyaltsen sun bayyana ra'ayoyi kan batutuwan da abin ya shafa, kuma sun ce za su ba da rahoto ga Dalai lama yadda ya kamata.

Mr. Zhu Weiqun da Mr. Sitar sun amsa tambayoyin da Mr. Lodi Gyari ya gabata,, kuma sun yi musanyar ra'ayoyi tare da shi da Mr. Kelsang Gyaltsen wajen sake tuntubar juna.

A ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da manema labaru na kafofin watsa labaru na kasar Japan da ke kasar Sin, ya ce, yana fatan bangaren Dalai lama ya daina yin aikace-aikacen nema ballewa daga kasa, da shirya aikace-aikacen ta da manyan laifuffuka, da lalata wasannin Olympics na Beijing a zaihiri, ta haka domin kirkira sharadi mai kyau ga shawarwarin nan gaba.