Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 16:58:07    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Wani manomi ya zama maalamin koyarwa a jami'a. Wani manomi ya zama malamin koyarwa a jamia bayan da ya yi karatu shi kansa na tsawon shekaru arba'in.Wannan manomi ya zo ne daga yankin Harbi na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Sunansa Qu Weijun, yana da shekaru 54 da haihuwa.Ya yi karatu a makarantar firamare kawai bai ci gaba da karatunsa a makaranta ba sabo da talaucin da iyalinsa ke fama da shi,,shi ya sa ya ci gaba da karatunsa shi da kansa har ya kware a fannin adabi na kasar Sin. Da aka samu labarinsa, jami'ar horar da malaman koyarwa ta birnin Harbin ta gayyace shi da ya zama malamin koyarwa a jami'ar.Daga baya dai wasu jami'o'I guda hudu su ma sun gayyace shi da ya yi koyarwa a makarantunsu.

Wata yarinya ta tsumbure saboda iyayenta sun kashe aure. Wata yarinya mai yawan shekaru 12 da haihuwa ta tsumbure a cikin shekaru hudu bayan da iyayenta suka kashe aure a birnin Shenyang na lardin Liaoning na kasar Sin. Sunan yarinyar Xiao Li,tsawonta bai kai centmeter 120 ba, ita ce mafi gajarta a cikin abokanta. Tsawon iyayenta kamar na sauran iyaye suke.Tun lokacin da iyayenta suka kashe aure,sai ran Xiao Li ta lalace sosai. Wani likita ya ce bacin rai ne ya kawo mugun tasiri ga kwayoyin halittar jikinta,wannan shi ne sanadin da Xiao Li ta tsumbure. Halin fara'a da hanyar zama mai kyau kamar su yin barci sosai da wasannin motsa jiki su ne ke taimakawa yaran su iya girma yadda ya kamata.

Karatun abubuwan gargajiya na iya taimakon shimfida yayin zamatakewa. Bisa labarin da aka samu daga lardin Shanxi na kasar Sin.An ce karatun adabi na gargajiya na iya kyatata zaman mazaunan birnin Taiyuan na lardin Shanxi na kasar Sin. Sabo da haka aka kaddamar da wani kamfen na karatun adabi na gargajiya na kasar Sin.Ga misal;I akwai abubuwa kamar bayanai daga darikar Confucius da three character Classic da nazarin hanyoyin da ya kamata a bi a zaman yau da kullum,Wannan ya kawo wani yanayi na da'a a wannan bangare.Daga bisani mutane masu dimbin yawa suna sha'awar karanta adabin gargajiya na kasar Sin musamman yara manyan gobe.

Wani nakasasshe ya zama mai gadi a wata unguwa ta birnin Beijing. Wani nakasasshe ya zama mai gadi a unguwar Erlizhuang ta birnin Beijing bayan da ya yi ritaya.Sunan nakasasshen shi ne Fei,yana da shekaru 65,ya kafa wani tsarin sa ido wanda ya hada da abin daukar hoto da amsa-kuwwa a aunguwar da yake zaune.Ko wace rana yana kula da tsarin sa ido domin tabbatar da zaman lafiya a gunguwa.Da ya ga wani bakon da ya bullo a unguwar da yake tsaron,sai ya yi masa tambaya daamsa-kuwwa,, idan ya amsa daidai ya bar shi ya ci gaba da tafiya a unguwar. Ta tsarin sa ido, an kama wasu barayi dake neman satar kekuna masu hawa.Mazaunan unguwar sun ce suna zama cikin kwanciyar hankali sabo da tsarin sa ido da aka shimfida.

---Wani mutum ya gabatar da gidan cin abinci a gaban kotu. Wani mutum ya gabatar da gidan cin abinci a gaban kotu sabo da gidan ya nneme shi da biyan kudin chopsticks da aka taba yin amfani da su.Mutumin nan shi ne Mr Zang. A watan jiya ne shi da abokansa biyu suka tafi gidan cin abinci.Bayan da suka gama cin abinci,sai suka biya kudin,da ya ga kudin chopsticks a cikin takardar rracidi, saiya yi fushi sabo da chopsticks da suka yi amfani da su,shopsticks ne da aka taba yin amfani da su,bai kamata a neme su sake biyan kudi ba.A ganinsa ba daidai ba ne.amma mai gidan cin abinci ya ce wannan ka'ida ce ake bi kullum a gidan nan na cin abinci.Daga bisani Mr Zang ya gabatar da gidancin abinci a gaban kotu.Wani alkali ya ce idan gidan cin abinci ya nemi a biya kudin chopsticks sai ya sanar da masu cin abinci kafin su ci abinci.Ana ci gaba da shari'ar batun .

----Wani direban babbar mota ya ba da taimako wajen kare mujiyoyi. Wani direban babbar mota na birnin Shijiazhuang na lardin Hebei dake arewancin kasar Sin ya ceci wata mujiya da ta samu rauni ta boye a cikin wani bangaren motarsa. Da direban ya ga mujiya ta boye a cikin motarsa sai ya so ya taimake ta da ta fita.Mujiya ta ki ta fita amma daga baya ya gane mujiya ta samu rauni. Mujiya na daga cikin manyan tsuntsaye da ba a safai ake ganinsu ba a kasar Sin ,shi ya sa gwamnatin ta kafa ka'idoji domin kare su.Tare da taimakon sauran ma'aikata,ya fitar da mujiyar ya kai ta cibiyar kula da dabbobi domin yi mata jinyya.

---Hukuma ta dauki matakin tsarkake harkokin aure. Wata hukumar kula da harkokin jama'a ta birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin ta bayar da wata takarda wadda a ciki ta bayyana cewa kada a yi amfani da kalmomi kamar su "mai kudi" ko "kyakkyawar budurwa" a cikin bayanan neman auren da aka buga a cikin jaridu da mijallu.An bayar da wannan takarda ne tare da nuna kawar da zambar da ake yi cikin harkokin neman aure da daidaita maganganun da ake amfani da su a wannan fannin .Duk wata hukumar da ta karya ka'idodin da aka tanada a cikin takardar,za a ci mata tara ko soke takardar lasisi da kawar da ita daga harkar gaba data.

----Kogunan duwatsu sun zama wurin shakatawa. An samu wasu koguna a cikin duwatsu biyu dake cikin gundumar Linzhou na lardin Henan na kasar Sin sabo da akwai ji sanyi a cikin kogunan a yanayin zafi, kuma akan ji zafi a cikinsu a yanayin hunturu,shi ya sa mutane masu yawan gaske daga gida da kasashen waje sun zo wurin domin ganin abin mamakin da aka samu da kuma shakatawa. Ya zuwa yanzu ba a gane dalilin da ya sa aka sami haka a wadannan kogunan duwatsu ba. Wasu kwararru suna tsammani asirinsu a karkashin kasa ne. Gwamnatin wurin ta yi shirin zuba mankudan kudare wajen mai da wurin shiyyar shakatawa mai shahara a kasar Sin. Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin. (Ali)