Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-14 18:02:26    
An fara kwantar da bala'i a kudancin kasar Sin

cri

A gun wani taron manema labarai da aka kira a yau 14 ga wata a nan birnin Beijing, wani jami'in sashen da abin ya shafa na kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu Sin ta cimma wasu nasarori wajen yaki da bala'in dusar kankara mai tsanani a kudancin kasar Sin, kuma jama'ar da ke yankunan da bala'in ya shafa suna cikin kwanciyar hankali, a yayin da kasuwanni ke gudana yadda ya kamata. Sassan da abin ya shafa na kasar Sin za su ci gaba da taimakawa jama'ar da bala'in ya galabaitar, da kuma gudanar da aikin farfado da gidajen da suka rushe a yankunan da bala'in ya shafa.

A gaban bala'i mai tsanani na matukar sanyi da dusar kankara da ya galabaitar da kudancin kasar Sin, sassan da abin ya shafa na kasar Sin da kuma yankunan da bala'in ya shafa suna iyakacin kokarin yaki da bala'i, da kuma tabbatar da zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata. A gun taron manema labarai da aka yi yau a nan birnin Beijing, Mr.Li Liguo, mataimakin ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin ya bayyana sabon ci gaba da Sin ta samu wajen yaki da bala'i, ya ce,"bisa kokarin da bangarori daban daban suke yi, an cimma babbar nasara wajen yaki da bala'in dusar kankara a kudancin kasar Sin, an tabbatar da biyan bukatun kasuwannin yankunan da bala'in ya shafa da kuma samar da kayayyakin agaji yadda ya kamata. A yanzu haka dai, jama'ar da ke yankunan da bala'in ya shafa suna cikin kwanciyar hankali, kuma kasuwanni na gudana yadda ya kamata."

Tun daga tsakiyar watan Janairu da ya gabata, bala'in dusar kankara mai tsanani ya afkawa wasu yankunan kasar Sin, kuma har zuwa lokacin da muke wannan bayani, mutane 107 sun mutu sakamakon bala'in, a yayin da wasu 8 suka bace. Bayan haka, an kuma sha hasarori har fiye da kudin Sin yuan biliyan 110 a fannin tattalin arziki. Bayan aukuwar bala'in, bi da bi ne sassan da abin ya shafa na kasar Sin suka yi jigilar rigunan auduga kusan miliyan 2 tare kuma da dimbin rumfuna da sauran kayayyakin agaji zuwa yankunan da bala'in ya galabaitar, bayan haka, gwamnatin kasar Sin ta kuma ware kudin Sin kimanin biliyan 2 da miliyan 700, don tsugunar da jama'ar da bala'in ya galabaitar. Ya zuwa yanzu dai, ba a sami bullar manyan cututtuka masu yaduwa da kuma matsalolin kiwon lafiyar jama'a a yankunan ba.

Amma duk da haka, Mr.Li Liguo ya kuma kara da cewa, sakamakon bala'in, dimbin gidajen kwana na jama'a da kuma aikin gona sun lalace, sabo da haka, ana ci gaba da daukar babban nauyi a wajen farfadowa da yankunan. Ya ce,"za mu ci gaba da gudanar da aikin yaki da bala'i da tabbatar da biyan bukatun kasuwanni, kuma za mu yi iyakacin kokarin taimakawa jama'a wajen daidaita matsalolinsu. A sa'i daya kuma, za mu fara aikin farfado da gidajen da suka wargaje tun da wuri, da kuma samar da jiyya cikin lokaci, sa'an nan, za mu tallafawa jama'ar da bala'in ya shafa da su farfado da aikin kawo albarka, ta yadda za a tabbatar wa jama'ar da bala'in ya shafa samun abinci da rigunan sa da ruwan sha da gidajen kwana da kuma jiyya, haka kuma yara na iya samun karatu, sa'an nan, a tabbatar da zaman rayuwar jama'a da kuma biyan bukatun kasuwanni a yankunan da bala'in ya galabaitar."

Bala'in ya kuma lalata aikin gona kwarai da gaske. Madam Zhang Yuxiang, wata jami'ar da abin ya shafa a ma'aikatar gona ta kasar Sin ta bayyana cewa, don tallafa wa jama'a da su farfado da aikin kawo albarka, sassan aikin gona sun riga sun share fage sosai, ta ce,"dangane da bala'in, muna dukufa kan yaki da bala'in da kuma farfadowa bayan bala'in, haka kuma muna dukufa kan bunkasa ayyukan gona daban daban daga dukan fannoni kuma cikin dogon lokaci."(Lubabatu)