Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-02 20:03:22    
Ya kamata hukumomi daban daban su kula da ayyukan fama da bala'i tare da nuna halin sauke nauyi bisa wuyansu kan moriyar jama'a

cri
Kwanan baya, daya bayan daya zaunannun mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin Mr. Li Changchun, da Mr. Li Keqiang, da kuma Mr. He Guoqiang sun yi bincike a jihohin Hubei da Sichuan da kuma Jiangxi, wadanda suka fi fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara. Kuma wadannan shugabanni sun jaddada cewa, ya kamata wurare daban daban, da kuma hukumomin da abin ya shafa su kula da ayyukan fama da bala'i sosai tare da nuna halin sauke nauyi bisa wuyansu kan rayuwa da dukiyoyi na jama'a, domin tabbatar da gudanar da tattalin arziki kamar yadda ya kamata.

A lokacin da suke yin bincike, wadannan shugabanni sun jaddada cewa, ya kamata a kula da fasinjojin da aka tsayar a tashoshin jiragen kasa da na motoci cikin lokaci, da kuma gudanar da ayyukan ba da tabbaci a fannonin samar da kwal, da wutar lantarki, da kuma sufuri, bugu da kari kuma a yi iyakacin kokari don warware matsalar kawo albarkatu da zaman rayuwa da jama'a masu fama da talauci ke fuskanta, ta yadda za a rage hasarar da bala'in ke kawowa zuwa matsayi mafi kankanta. (Bilkisu)