Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-02 17:04:20    
Wasu shugabannin kasashen duniya sun nuna jaje ga Sinawa masu fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara

cri
A kwanan baya, bi da bi ne wasu shugabannin kasashen duniya suka aiko wa shugaba Hu Jintao da firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin sakwanni, inda suka nuna jaje domin ci gaba da kasancewa cikin hali mai tsanani sosai wajen fama da bala'in ruwan sama da dusar kankara a wasu yankunan kudancin kasar Sin.

Wadannan shugabannin kasashen duniya sun hada da Mr. Kim Jong Il, babban sakataren kwamitin tsakiy na jam'iyyar 'yan kwadago ta Koriya ta arewa, kuma shugaban kwamitin tsaron kan kasar da Mr. Choummaly Saygnasone, shugaban kasar Laos da firayin ministan kasar Mr. Bouasone Bouphavanh da shugaban kasar Koriya ta kudu Roh Moo Hyun da shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf. A cikin sakwaninsu, sun nuna jaje ga gwamnatin kasar Sin da Sinawa wadanda suke fama da bala'i, kuma sun nuna musu tausayi. A waje daya kuma, sun yaba wa gwamnatin kasar Sin domin ta yi namijin kokari wajen maido da zaman rayuwar jama'a kamar yadda ya kamata. Sun amince da cewa, tabbas ne gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar za su iya samun nasarar fama da bala'i tun da wuri. (Sanusi Chen)