Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-12 15:41:32    
Idan yara su kallo TV da yawa, za a yi musu mugun tasiri ga hankulansu a lokacin balaga

cri
Kwanakin baya, 'yan kimiiya na kasar New Zealand sun bayar da wani rahoto kan sakamakon nazarin da suka samu, inda aka ce, idan tsawon lokacin da suka kashe wajen kallon TV ya kai awo'i biyu a ko wace rana, sai bayan da su shiga lokacin balaga, mai yiyuwa za su kamu da matsalar rashin mai da hankulansu kan abubuwa.

Mr. Carl Landhuyi 'dan kimiyya na wata jami'ar kasar New Zealand ya bayar da wani rahoto cikin "mujallar kimiyya ta 'yara" ta kasar Amurka, inda ya ce, duk yaro da yarinya, idan tsawon lokacin da suka kashe wajen kallon TV ya kai awo'i biyu a ko wace rana, sai yiwuwar da za su kamu da matsalar rashin mai da hankulansu kan abubuwa za ta karu da kashi 40 cikin 100.

Mr. Landhuyi da sauran 'yan kimiyya sun sami wannan sakamako bayan da sun binciken mutane fiye da dubu daya na kasar New Zealand wadanda aka haifisu daga watan Afrilu na shekarar 1972 zuwa watan Maris na shekarar 1973.

Game da haka, Mr. Landhuyi ya bayyana cewa:

Da farko, kullum ana canja hotunan shirye shirye da yawa na TV da sauri, wannan zai yi mugun tasiri ga hankalin yara, saboda hankulansu ba su balagagge ba.

Na biyu, idan su kashe lokaci da yawa kan kollon TV, dole ne ba za su yi sauran ayyuka kamar karanta, da motsa jiki da wasanni wadanda za su koyar da musa mai da hankulansu ba.

yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani kan hadarin kamu da illar hauhuwar jini, idan yara su kashe lokaci da yawa wajen kallo TV.

Bisa sakamakon nazarin da 'yan kimiyya na kasar Amurka suka yi a kwanakin baya, idan yara su kashe lokaci da yawa wajen kallo TV, to, ban da za su sami kiba, haka kuma za su fuskantar da hadarin kamu da illar hauhuwar jini.

A cikin wannan rahoton da aka bayar a mujallar "ilmomin yin rigakafi" na kasar Amurka, tun daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2005, 'yan kimiyya na jami'ar jihar California ta kasar Amurka sun yi bincike ga 'yara masu kiba 546 a dogon lokaci domin sanin tsawon lokacin da suka kashi wajen kallon TV, kuma sun kwatanta tsayin jiki, da nauyin jiki, da kuma matsin jini na su.

Bisa sakamkon binciken da suka yi, yawan 'yara masu kiba da suka kamu da illar hauhuwar jini wadanda suka kashe awo'i 2 zuwa 4 wajen kallon TV ya ninka sau 2.5 bisa na 'yara masu kiba wadanda ba su kallo TV ko tsawon lokacin da suka kashe wajen kallon TV bai kai awo'i 2 ba, kuma yawan 'yara masu kiba da suka kamu da illar hauhuwar jini wadanda suka kashe awo'i fiye da 4 wajen kallon TV ya ninka sau 3.3 bisa na 'yara masu kiba wadanda ba su kallo TV ko tsawon lokacin da suka kashe wajen kallon TV bai kai awo'i 2 ba.

Kafin wannan kuma, an riga an shaida cewa, idan 'yara su kallo TV da yawa sosai, mai yiyuwa ne za su sami kiba. Masu bincike suna ganin cewa, game da 'yara masu kiba, suna bukatar rage tsawon lokacin da suka kashe wajen kallon TV, kuma ya kamata duk iyaye, da likitoci da masu ba da agaji su mai da hankulansu kan wannan batu.