Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-07 12:45:07    
Sabuwar manufar daidaitawa ta kasar Sin na da amfani ga ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar kamar yadda ya kamata

cri

An labarta cewa, shekaranjiya ne, aka kawo karshen taron kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kan harkokin tattalin arziki, wanda aka gudanar da shi domin aza tubali mai inganci ga bunkasa tatttalin arzikin kasar gadan-gadan. Taron fafau ya fito da cewa, a shekara mai kamawa, gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar da manufar kudi kamar yadda ya kamata yayin da take tsuke bakin aljihunta domin jan birki ga saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da kuma magance tsawwalar farashin kaya.

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, kasar Sin ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2007. An yi kiyasin cewa, jimlar GDP da aka samu daga aikin kawo albarka a wannan shekara ta kai kimanin kashi 11.5 cikin kashi 100 idan aka kwatanta ta da ta shekarar bara. Amma, har ila yau dai,gwamnatin kasar Sin na fama da wassu matsaloli yayin da take gudanar da harkokin bunkasa tattalin arziki, alal misali : ana ta samun karuwar yawan kudin da aka zuba domin samun kadadori fiye da kima, sa'annan yawan rancen kudin da ake zubawa ya yi yawan gaske ; kazalika, yawan kudin da akan samu daga cinikin shigi da fici yana karuwa sosai. Musamman ma, ana kara samun karfin matsi daga tsawwalar farashin kaya a shekarar da muke ciki. Daidai bisa wannan yanayi ne, taron ya jaddada cewa ya kamata a mayar da aikin kayyade saurin bunkasuwar tattalin arziki da na magance raguwar darajar kudi sakamakon tsawwalar farashin kaya a matsayin aiki na farko na ayyukan daidaita harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni. Mr. Yuan Gangming, darakatan ofishin nazarin tattalin arziki na kwalejin zamantakewar al'umma da kimiyya ta kasar Sin ya furta cewa : 'Da yake mun samu karuwar tattalin arziki sosai cikin shekaru biyar a jere yayin da muka samu GDP da yawansa ya zarce kashi 11 cikin kashi 100 a wannan shekara, shi ya sa muka samu damar warwarre wassu wahalhalun da muka gaza wajen daidaita su cikin dogon lokaci. Amma karuwar tattalin arziki fiye da kima, kila za ta haifar da raguwar darajar kudi ; Ban da wannan kuma, yawan kudin da mazauna biranen kasar suka kashe wajen sayen kayayyaki ya karu cikin hanzari. To, lallai mutane na shakkar cewa ko hakan zai haifar da tsanancewar tsawwalar farashin kaya ? Ko shakka babu za mu yi kokarin riga-kafin aukuwar lamarin. '

Bugu da kari, taron ya tsaida kudurin aiwatar da manufar kudi gadan-gadan da kuma tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar tun daga shekara mai zuwa. Game da wannan dai, wani kwararre a fannin kudi mai suna Yi Xianrong yana mai cewa : ' Yanzu, kwamitin tsakiya na JKS ya riga ya gane sosai cewa, an samu karuwar tattalin arziki cikin hanzari fiye da kima. Babu tantama, manufar tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar za ta taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsalar zuba jari da kuma samar da rancen kudi mai yawan gaske ba kamar yadda ya kamata ba'.

A yayin da Mr. Yi Xianrong yake tabo magana kan manufar kudi da gwamnatin kasar za ta aiwatar da ita gadan-gadan, ya fadi cewa: " Rahoton babban taro na 17 na kwamitin tsakiya na JKS da aka gudanar a wannan shekara ya shafi wani batun yalwata muhimman ayyukan hidimomi domin jama'a. Saboda haka, za a fi mayar da hankali kan yadda za a aiwatar da manufar kudi a shekara mai zuwa. A takaice dai, za a yi namijin kokari wajen daidaita maganar zaman rayuwar jama'a ta fuskar samar da kudi".

Mr. Yuan Gangming shi ma ya yarda da ra'ayin Malam Yi Xianrong. Cewa yayi, manufar kudi da za a aiwatar a shekara mai zuwa, wata irin manufar kudi ce dake mai da hankali kan fa'ida da moriya da za a samu bisa matsayin daidaici. Ya kuma kara da cewa: " Ya kamata a kara zuba makudan kudade a fannin bada ilmi, da aikin jinya da kuma na sha'anoni domin jama'a da dai sauran fannoni. Musamman ma a fi mai da hankali kan zuba jari zuwa yankuna dake fama da talauci da kuma kauyuka, ta yadda za a bada taimako ga kyautata harkokin tattalin arziki ta hanyar samar da kudi daga gwamnatin kasar".( Sani Wang )