Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 17:23:25    
Cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan aikin sake amfani da tsohuwar wayar salula.

Manazarta na kasar Jamus sun bayar da wani rahoto a kan mujallar kungiyar aikin likitanci ta kasar Amurka, cewa sakamakon nazari da suka yi ya bayyana cewa, cin bakar cakulan kadan a ko wace rana zai iya rage hauhawar jini.

Kafin wannan, wani nazarin da aka yi ya taba shaida cewa, sabo da bakar cakulan tana kunshe da sinadarin polyphenols, shi ya sa take iya rage hauhawar jini. Amma wasu kwararru sun nuna damuwa cewa, idan ana cin bakar cakulan da yawa fiye da kima, yawan sukari da kitse da calorie da za a samu zai kawo cikas ga amfanin bakar cakulan wajen rage hauhawar jini.

Sabon nazarin da manazarta na asibitin da ke karkashin jami'ar Koeln ta kasar Jamus suka yi ya tabbatar da cewa, idan ana cin bakar cakulan kadan kamar mai yawan kusan gram 6.3 a ko wace rana, za a iya samun raguwar hauhawar jini ba, kuma ba zai haddasa karuwar nauyin jiki da kuma sauran amfani maras kyau ba.

Manazarta sun gudanar da wannan bincike ga mutane 44 da shekarunsu ya kai 56 zuwa 73 da haihuwa, wadanda dukkansu suke da hauhawar jini a matsayi daban daban, kuma ba su taba yin jiyya ba. A cikin wannan bincike na makwanni 18, an kasa wadannan mutane cikin rukunoni biyu ba tare da yin zabi ba. Mutanen da ke wani rukuni sun ci bakar cakulan gram 6.3 a ko wace rana, yayin da mutanen da ke dayan rukuni suka ci farar cakulan wadda ba ta kunshe da sinadarin polyphenols gram 6.3 a ko wace rana. Daga baya kuma sakamakon binciken ya gano cewa, game da wadanda suka ci bakar cakulan, karfin bugun jini nasu na sama ya ragu da millimeter 2.9 bisa ma'aunin bugun jini, yayin da karfin bugun jini na kasa ya ragu da millimeter 1.9, amma karfin bugun jini na wadanda suka ci farar cakulan bai canja ko kadan ba.

Manazarta sun bayyana cewa, ko da yake ba a iya samun raguwar hauhawar jini sosai ta hanyar cin bakar cakulan ba, amma ya fi kyau a mai da hankali a kan sakamakonsa wajen jiyya. Bisa sakamakon nazarin likitancin da aka yi, an ce idan karfin bugun jini na sama ya ragu da millimeter 3, to hadarin mutuwa sakamakon shanyewar jiki zai ragu da kashi 8 cikin dari, haka kuma hadarin mutuwa sakamakon cutar toshewar jijiyoyin jini na zuciya zai ragu da kashi 5 ciki dari. Ban da wannan kuma, cin bakar cakulan kadan a ko wace rana wani abin sauki ne ga mutanen da ke fama da hauhawar jini, ba a bukatar canja al'adarsu wajen cin abinci sosai ba.

Amma a waje daya kuma manazarta sun nuna cewa, ana bukatar ci gaba da yin nazari domin tabbatar da cewa, ko sakamkon da muka ambata a baya ya dace da sauran mutane. Haka kuma ya zuwa yanzu ba a san tsawon lokaci na amfanin cin bakar cakulan wajen rage hauhawar jini ba.