Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 17:17:23    
Wani babban malamin da ke da fasahar yin zane-zane kan kayayyakin fasahar hannu mai suna Zhang Tonglu

cri

Jingtailan shi ne wani kayan fasahar hannu da ya sami suna sosai a kasar Sin, yana da dogon tarihi, kuma ana kera shi ta rikitattun hanyoyi iri iri da yawa. Malam Zhang Tonglu shi kadai ne ya zama babban malamin da ya rike da dukkan fasahohin kera Jintailan a kasar Sin, shi ya sa ana kiransa cewar, mutumin farko na kera Jintailan na kasar Sin.

Jintailan shi ne wani kayan fasahar hannu da kasar Sin ita kadai take iya kera shi, ana yin amfani da fasahar hada da tagulla da tangaram wajen kera shi tare da yin zane-zane a kai da sassaka shi da hannu kawai bisa fasahar musamman ta gargajiyar kasar, fasahar kera Jintailan tana hade da dukkan fasahohin gargajiya na kera kayayyakin fasahar gargajiyar kasar Sin. Dayake an soma yin amfani da fasahar a shekarun sarkin Jintai na daular Ming a tsakiyar karni na 15 , kuma yawancin kayayyakin an kera su ne da launin shudi, wato da harshen Sinanci ake cewa, Lan ke nan, shi ya sa ake kiran irin kayan da cewa, Jingtailan.

A shekarar 1958, Mr Zhang Tonglu ya cika shekaru 16 da haihuwa, kuma ya yi kishin yin zane-zane sosai .A wata rana ,ya ga wata takardar tallace-tallacen sinima wadda a cikinta da akwai wani zanen da aka yi dangane da wani tsoho mai yin zane-zane na ma'aikatar kera kayayyakin Jintailan da ya ke yin zane-zane a kan kayan Jintailan, shi ya sa malam Zhang Tonglu ya tsai da kudurin neman aiki a ma'aikatar, sa'anan kuma an dauke shi, amma da ya shiga aiki a ma'aikatar, sai ya gane cewa, da muka shiga cikin ma'aikatar, da farko mun yi aikin kera danyun samfurorin mutum mutumi, wato mun yi amfani da zare-zaren tagulla don saka su da su yi kama da samfur wani kanya, har na yi samfurorin kwanuka ko kwalabe cikin shekara daya. Wani tsohon hannu ya ga kayayyakin da na kera, sai ya gaya mini cewa, abin da na yi da kyau, ya kamata zan ci gaba da kokari, kuma makomata na da kyau. Da na tambaye shi cewa, ko a wane lokaci zan iya soma koyon fasahar yin zane-zane a kan kayan Jingtailan? Sai ya gaya mini cewa, saurayi, watakila ba za ka iya kwarewa ba a duk zaman rayuwarka, kuma ba za ka iya koyon sauran fasahohin kera Jintailan ba. Da jin maganarsa, sai na ji sanyi a zuciyata, na yi shakka cewa, wane lokacin ne da zan iya koyon fasahar yin zane-zane?

A gaskiya dai aka sami Jintailan ba dole ne a bi hanyar yin zane-zane kawai ba, ana bin hanyar tsara fasali da saka samfurori ta hanyar yin amfani da tagulla da gasar da su da dai sauran ayyuka iri iri fiye da goma, a lokacin aikin kera Jingtailan, wani ma'aikaci ya iya kulawa da wani kashin aikin kawai, kuma watakila ya yi wannan aiki a wajen kashi daya kawai har a duk rayuwarsa, Amma Mr Zhang Tonglu ba ya son yin aiki wajen kashi daya kawai ba, yana son yin zane-zane a kan Jintailan da sauransu.

Don cim ma burinsa, sai Zhang Tonglu ya shiga karatu a makarantar koyar da fasahohin yin zane-zane kan kayayyaki ta birnin Beijing. Yana kokarin karatu, ya rike da ilmin tsara samfurorin kayayyaki da daidaita launuka da sauran ilmi dangane da fasahar yin zane-zane. Bayan da ya sauke karatun, sai ya sake shiga aiki a ma'aikatar da ya taba aiki, ya zuwa lokacin, ma'aikatar ta riga ta sami bunkasuwa, har ta zama wani sansani mafi girma wajen fitar da kayayyakin fasahar gargajiya.

1 2