Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-27 15:54:26    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

---An kama wani mutum sabo da ya jefa kwalba ta taga:wani mutum da ya zama a wurin San Po na yankin mulkin musamman na Hongkong ya kan goge injin sanyaya yanayi wato air-conditioner a turance da ruwan tsami,wata rana bayan ya goge injin ya ga babu ruwan tsami mai yawa a cikin kwalba,sai ya jefa kwalbar ta taga,ashe ruwan tsamin dake cikin kwalba ya fita yayin da ake jefawa har ma jawo rauni ga matafiya guda goma sha hudu a kan hanyar dake karkashin ginin da wannan mutum ya ke zaune.Daga baya 'yan sanda sun zo sun tambayi wane ne ya aikata wannan mugunta ba wanda ya ba da amsa.'yan sanda sun yi bincike dalla dalla,sun duddubi hanyar da kwalbar take bi da kuma ruwan tsami da ta fesa,daga baya 'yan sanda sun gano dakin da mai aikata laifi ya ke zaune,sun kuma samu dukkan shaidun da suka tabbatar da laifin da ya yi.mutumin nan ya amsa laifi.'yan sanda sun kama shi.

----An tsare samari guda biyu sabo da suka ta da fitina da waya.An tsare samari biyu a Macao sabo da suka buga wayoyi ga ofishin 'yan sanda,wannan laifi ne a Macao ana iya sa mutum da ya aikata laifin nan cikin gidan wakafi na shekara daya. Wani jami'in 'yan sanda ya ce wani saurayi mai suna Wang ya samu waya a ran 29 ga watan Yuni,wayar ta dame shi kawai ba don kome ba,sai nan da nan ya mayar da wayar zuwa ga 2255---7777,wata hanyar waya (hot line) ta ofishin 'yan sanda.Ya maimaita haka sau da yawa har ma yayin da buduwarsa ta buga masa waya,ya kuma koya wa budurwa hanyar da yake bi.Daga baya 'yan sanda sun bi bahasin waya,suka same su biyu.'yan sanda sun tsare samarin.

---Wata mata ta cuci abokanta da kudin dalar Hongkong miliyan 1.2.Wata mata mai kishin zagaya kantuna ta cuci abokanta da kudin dalar Hongkong miliyan 1.2 domin saye takalmi.An yi mata shari'a a ranar laraba da ta gabata a Hongkong.Mai aikata laifi sunanta Yuan,tana da shekaru talatin da haihuwa.tana aiki a bank.Ta yi ikirari cewa tana da wani shirin zuba jari tare da ruwan kudi mai tsoka.Yuan tana da wani aboki da ta san shi sama da shekaru goma,ta ce idan ya ba ta kudin dallar Hongkong dubu 850,za ta mayar masa da kudin dalar Hongkong dubu 960,abokinta ya amince ta ya ba ta kudin da take bukata.Kamar yadda ta yi da abokinta,haka ma ta yi ga saura,bayan watanni uku da wa'adin ya cika ta kasa mayar da adadin kudin da ta yi alkawarin.Aka gabatar da ita a gaban kotu,ta amsa laifin,ta ce ta yi amfani da kudin da ta samu daga abokanta wajen saye takalmi da biya bashin da ta ci.Bank ya sallame ta,aka sa ta cikin gidan wakafi.

----66% mata a Hongkong ba su so su yi ritaya.kashi biyu bisa kashi uku na mata a Hongkong sun yi alfahari da matsayin yancin da suke rike da shi a fanning kudade,duk da haka ba su so su yi magana kan shirinsu na yin ritaya.Wannan sakamako ne da aka samu bayan da kungiyar jama'a ta taimakon juna da jami'ar Hongkong dake amfani da harshen sinanci suka yi.Daga cikin mata fiye da 720 da aka yi musu tambayoyi cikin bincike,kashi 66 bisa dari sun ce suna da 'yanci wajen amfani da kudi.kashi 14 bisa dari sun ce kamata ya yi su yi shiri wajen amfani da kudi bayan da suka yi ritaya.kashi 58 bisa dari sun ce kudin da suke amfani da shi ya ragu da rabi bayan ritaya.Sakamakon binciken ya kuma yi nuni da cewa kashi 60 na matan Hongkong ba su zuba jari kan ayyuka ba banda asusun kudin fenshon da aka tanada dominsu.

----wata budurwa ta samu amincewa.Wata budurwa dake shekaru 26 da haihuwa,da tsawonta ya kai mita 1.8 ta samu amincewa bayan da aka dauke ta a matsayin ma'aikaciya ta gwamnati sabo da rawar da ta taka a cikin bikin nuna tufafi na sabon salo.Sunan budurwa ita ce Zuo Lei ta zo ne daga birnin Xianyang na lardin Sha'anxi.ta kan sa hankalinta kan tsawonta sabo da yawancin matan kasar Sin tsayinsu bai kai nata ba.Budurwar ta ce bayan da ta kammala karatunta a makaranta tana so ta samu aikin yi a wani hotel,amma hotel ba ya dauke ta ba bisa dalili na cewa ta fi sauran 'yan mata tsayi sosai.shi ya sa ta yi kokarin rage tsawonta ta dabaru iri iri.A shekara ta 2002,makarantar horar da kyakkyawan mata ta dauke ta bayan da ta yi karatu ta shiga wani bikin nuna kyakkyawan mata da gidan rediyo mai hoto na lardin ya shirya a shekara ta 2003 har ta samu nasara.niyyarta ma ta kara karfi.wata ma'aikatar gwamnati ta kuma dauke ta a wannan shekara.Daga nan ta zama ma'aikaciya,duk da haka ta kan shiga bikin nuna kyakkyawan matan da aka shirya bayan lokacin aiki.

----Wani injiniya ya yi ritaya domin kula da ubansa. Wani injiniya a birnin Xian na lardin Shaanxi wanda yana samun albashi mai tsoka yau daura niyyar yin ritaya domin kula da ubansa da ya ke fama da cutar kanjiki.Injiniya ya ce likita ya gaya mini cewa kwanakin ubana ya kusa karewa.Ni dansa ne daya kawai a gida,kamata in raka shi yayin da yake raye.Sunan injiniyan shi ne Yan Feng,yana da shekaru 37 da haihuwa.Ubansa shekaru 62 da haihuwa,likitan ya gane ainihin cutar da ubansa ke fama ita cewa cutar kanjiki ta huhu ce,babu kwanaki da yawa da yake zama a duniya.A ganin Yan Feng,ya kamace shi da ya yi zama da ubansa kowace rana.

---An gano wasu tsire tsire da dabobi a wani kwari.An gano wani kwari mai tsawon kilomita goma ko fiye a gundumar Ningqiang na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.kwarin ne ya shimfidu a wani gandun daji na gundumar tare da koguna da kogwan dutse da dama.Bisa labarin da ma'aikatar gandun dajin suka bayar,an ce an kuma gano wasu sabbin tsire tsire da dabbobin da ba a taba ganin irinsu ba a wannan bangare.(Ali)