Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-09 16:50:29    
Aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa da ake yi a kasar Sin

cri

A ran 26 ga watan Satumba, an fara aikin kyautata mafarin ruwa na sashen tsakiya na babban aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa na kasar Sin wato aikin kara tsayin datsiyar matarin ruwa na Danjiangkou da gaske.

Da karfe 10 da minti 30 na wannan ranar da safe, Ning Yuan, mataimakin direktan ofishin aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa na majalisar gudanarwa ya yi shelar fara aikin kara tsayin datsiyar ruwa. Ya ce, "bayan da aka fara aiki na sashen gabas da na tsakiya a shekarar 2002 da kuma karshen shekarar 2003 bi da bi, bisa matsayin alamar aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa, aikin kara tsayin babbar datsiyar matarin ruwa na Danjiangkou ya alamanta cewa, aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa ya shiga wani matakin tafiyar da aikin daga duk fannoni."

Bayan da aka shafe shekaru 5 ana ta yin gine-gine, a karshe kuwa muhimminin aiki na sashen tsakiya na babban aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa wato babbar datsiyar matarin ruwa na Danjiangkou wadda za ta kara tsayinta da kusan mita 15, yawan ruwan da za a tattara cikin matarin ruwa zai karu da cubic mita biliyan 11.6, ta yadda za a iya samun tabbacin samar da cikakken ruwan da ake bukata ga arewacin kasar Sin a kowace shekara. Fadin matarin ruwa zai karu daga murabba'in kilomita 745 zuwa 1050, yawan kudin da aka ware domin aikin ya kai Renminbi fiye da Yuan biliyan 10.

Bisa babban shirin da aka tsayar kan aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa an ce, cikin shekaru 40 zuwa 50 masu zuwa, za a tsai da lokutai 3 don yin wannan aiki, jimlar ruwan da za a jawo daga kudu zuwa arewa zai kai cubic mita biliyan 44.8, jimlar kudin da za a ware domin aikin kuma zai kai Renminbi Yuan biliyan 486.

Aikin da ake yi yanzu aiki ne na lokaci na kusa wato daga shekarar 2002 zuwa ta 2010, jimlar ruwan da za a jawo cikin wannan lokaci zai kai cubic mita biliyan 20, daga cikin su da akwai cubic mita biliyan 9.5 wadanda za a jawo su ne daga matarin ruwa na Danjiangkou.

Za a karasa aikin kara tsayin babbar datsiyar matarin ruwa na Danjiangkou a shekarar 2010. A lokacin za a jawo ruwa daga wannan matarin ruwa wato mafarin kogin Yangtze da ke kudancin kasar Sin, ruwan zai bi ta babbar magudanar ruwa mai tsawon kilomita 1420, kuma zai ratsa kogin Huai da Rawayen kogi, har zai shiga cikin kwarin kogin Hai da ka arwancin kasar Sin.

Matsakaicin yawan albarkatun ruwan da kowane mutun ke mallaka a kasar Sin ya kai kashi daya cikin 4 kawai bisa na matsakaicin matsayin duniya. Fadin gonaki da yawan hatsin da aka samu da yawan mutane da kuma yawan GDP na kwarin Rawayen kogi da na kogin Huai da kogin Hai da ke arewancin kasar Sin dukansu sun wuce sulusi bisa na duk kasar, amma matsakaicin yawan albarkatun ruwan da kowane mutun ke mallaka ya kai kashi daya cikin 5 bisa na duk kasar kawai.

Bisa babban fasalin aikin jawo ruwa daga kudu zuwa arewa na kasar Sin an ce, bayan da aka kammala ayyuka daban-daban na babban aikin za a sassauta matsalar karancin ruwa da ake gamuwa da ita a larduna da jihohi fiye da 10 ciki har da birnin Beijing da na Tianjin, da lardin Henan da Shandong da ke arewacin kasar, da lardin Qinghai da na Gansu, da jihar Ningxia da ta Mongoliya ta gida, da lardin Shanxi da na Shanxi daga duk fannoni, wato za a jawo zaman alheri ga mutane fiye da miliyan 300 na kasar Sin. (Umaru)