Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 15:18:22    
Kungiyar ASEAN ta sami babban ci gaba a cikin shekaru 40 da suka wuce

cri

A ran 8 ga wata zagayowar rana ce ta cikon shekaru 40 da kafa Kungiyar ASEAN. A cikin shekaru 40 da suka wuce, kungiyar ta sami kyakkyawan sakamako a fannin siyasa da tatalin arziki da hadin kan shiyya-shiyya, ta ba da babban taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da zaman karko da wadatuwa a shiyyar kudu maso gabashin Asiya, kuma ta zama kungiyar kasa da kasa mafi muhimmanci a shiyyar kudu maso gabashin Asiya a yau, kuma tana daya daga cikin kungiyoyin shiyya-shiyya da ba za a iya kau da kai a kansu ba a duniya.

Kungiyar ASEAN ta kafu ne a shekarar 1967. Makasudin kafuwarta shi ne domin kara daga karfin kasashen shiyyar wajen cin gashin kai, da inganta hadin kansu a fannin tsaro, da samun daidaituwa a tsakaninta da kasar da ke neman nuna isa a shiyyar, da kiyaye zaman lafiyarsu da wadatuwarsu yadda suka ga dama. A farkon lokacin kafuwarta, kungiyar ASEAN ita ce wata kungiyar siyasa ta shiyya-shiyya, amma tana kara samun ci gaba wajen cim ma manufar hadin kan tattalin arzikinsu sannu a hankali.

Yanzu, a bangaren siyasa, ba ma kawai kullum Kungiyar ASEAN tana aiwatar da akidar zaman daidaici da hadin kai don sa kasashen kungiyar da su yi zaman tare cikin lumana ba, har ma ta kafa tsare-tsaren hadin kai na shiyya-shiyya wadanda kungiyar ke zaman ginshikinsu sannu a hankali, tana hadin kanta da manyan kasashen nahiyar Asiya da ta Amurka da Turai ta hanyar hadin kanta da kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu da yin taron kolin gabashin Asiya da sauransu, ta tabbatar da zaman alfiya da zaman karko da bunkasuwa da wadatuwa a duk shiyyar.

A fannin tattalin arziki, kasashen kungiyar ASEAN suna kokari wajen tabbatar da hadin kan tattalin arzikin shiyyar, don kara samun karfinsu. Ta hanyar kafa shiyyar cinikayya maras shinge ta kudu maso gabashin Asiya, kungiyar ba ta buga harajin kwastan a kan cinikayya da ake yi a shiyyar ba, kuma tana neman kafa kungiyar tarayyar tattalin arziki ta kudu maso gabashin Asiya kafin karshen shekarar 2015. Haka kuma kungiyar ta daddale yarjejeniyar yin cinikayya cikin 'yanci a tsakaninta da kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu da Indiya da Australiya da New Zealand da sauransu.

A fannin al'adu, mutanen kasashen kungiyar suna kara kai wa juna ziyarce-ziyarce, kuma suna kara inganta ma'amalar al'adu a tsakaninsu. Kasashen kungiyar sun rattaba hannu a kan "Sanarwa kan tsoffin kayayyakin al'adu na kungiyar ASEAN don kiyaye tsoffin kayayyakin al'adu na kungiyar cikin hadin guiwarsu.

Haka kuma A kwanakin baya, ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar ASEAN sun sami ra'ayi daya a kan daftarin "tsarin dokoki na kungiyar ASEAN", wannan babban ci gaba ne mai muhimmanci sosai da kungiyar ta samu a cikin tarihinta. Idan an rattaba hannu a kan daftarin tsarin nan, to, tsarin zai zama takardar bayani mai muhimmanci sosai ga tarihin kungiyar.

Lalle, kungiyar ASEAN ta gamu da matsaloli da yawa a kan hanyar samun ci gaba. Alal misali kurar da ta tashi a fannin siyasa na wasu ksashen kungiyar, kasashen kungiyar sun bunkasa harkokin tattalin arzikinsu cikin rashin daidaituwa, kuma suna fuskantar kalubale daga ta'addanci da cutar murar tsuntsaye da laifuffuka da ake yi a tsakanin kasa da kasa da sauransu. Sabo da haka kasashe daban daban na kungiyar suna ta yin shawarwari da tattaunawa a tsakaninsu ba tare da kasala ba, don neman kawar da sabanin ra'ayi da ke tsakaninsu da daidaita matsaloli, ta yadda za a kara kyautata tsare-tsaren kungiyar, da kara inganta hadin kansu don moriyar juna. A ran 7 ga wata, yayin da Mr Lee Hsien Loong, firayim ministan kasar Singapore ke bayar da jawabi kan ranar kungiyar ASEAN, ya ce, ya kamata, kungiyar ASEAN ta sa jama'a su amince da cewa, kungiyar za ta zama wata gadar da ake yin ma'amala a nahiyar Asiya, kuma za ta tasa muhimmiyar rawa cikin daidaici. (Halilu)