Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 08:27:03    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (01/08-07/08)

cri
Ran 6 ga wata,mataimakin shugabannin zartaswa biyu na kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na birnin Beijing Wang Wei da Jiang Xiaoyu sun bayyana cewa,ana gudanar da aikin share fage na taron wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 bisa shirin da aka tsara,kuma an riga an samu sakamako mai faranta ran mutane.Mataimakin shugabannin nan biyu sun kara yin bayani cewa,aikin gine-ginen dakuna da cibiyoyin wasannin Olimpic na Beijing yana tafiya kamar yadda ya kamata,aikin shirya gasanni shi ma yana tafiya kamar yadda ya kamta.Ban da wannan kuma,sharadin sufuri da muhallin hallitu masu rai da marasa rai na birnin Beijing suna samu kyautatuwa a kai a kai.

Ran 5 ga wata,a gun babban taron wakilan hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki na daliban jami`an kasashen duniya,`dan kasar Amurka George E.Killian ya samu kuri`un amincewa 84 da aka jefa ya ci zabe kuma zai ci gaba da zama shugaban kungiyar nan,mataimakin ministan ma`aikatar ba da ilmi ta kasar Sin Zhang Xinsheng shi ma ya ci gaba da zama mataimakin shugaban kungiyar.Yanzu hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki ta daliban jami`an kasashen duniya tana da mambobi 125,kuma ta shirya taron wasannin daliban jami`an duniya sau daya ne a duk shekaru biyu.Ana kiran taron da sunan `karamin taron wasannin Olimpic`.

Ran 5 ga wata,aka rufe gasar wasan kwallon kafa tsakanin kasashe hudu da aka shirya bisa gayyata a birnin Shenyang dake arewacin kasar Sin.A gun zagaye na karshe na gasar,kungiyar Olimpic ta kasar Korea ta arewa ta lashe kungiyar Olimpic ta kasar Sin,kuma kungiyar Olimpic ta kasar Botswana ta lashe kungiyar kasar Japan,a karshe dai,kungiyar Olimpic ta kasar Botswana ta samu zama ta farko wato ta zama zakara,kungiyar kasar Sin ta samu zama ta biyu a bayanta.Ban da wannan kuma kungiyar kasar Japan da ta kasar Korea ta arewa sun zama zama na uku da na lamba ta hudu.(Jamila zhou)