Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 15:28:39    
Kong Zi da darikar Confucius(B)

cri

Da akwai wani karamin littafin da ake kira Lunyu wanda yana daukar tunanin Confucius da maganganunsa da kuma take takensa.A cikin littafin nan an rubuta hasashen da Confucius ya yi da kuma zancen da ya yi da almajiransa.A zamanin can da a kasar Sin an dauki wannan littafi kamar littafi mai tsarki Bible a kasashen Yamma.Idan shi talaka ne ya kamata ya yi kome bisa abubuwan da aka tanada a cikin wannan littafi.Idan wani yana so ya samu mukami ya shiga harkokin mulki,kamata ya yi ya nazarci wannan littafin sosai. Da akwai wani karin magana a kasar Sin na cewa da rabin littafin Lunyu ka iya tafiyar da harkokin mulkin kasa,wannan yana nufin cewa idan ka samu rabin ilimin da littafin Lunyu ya kunshe,za ka iya tafiyar da harkokin mulkin kasa.

Wajen karatu Confucius ya ce kamata ya yi a yi karatu a ko wace rana kuma a aikata abin da aka koya.Yayin da kake karatu,sai ka yi tunani mi zurfi,in ba haka ba ba za ka samu ilimi ba.ya kuma ce idan ba ka so yi wani abu,kada ka nemi saura su yi wannan abu.Kan tafiyar da harkokin mulki Kong Zi ya ce idan ba ka kan kujerar mulki kada ka nemi damar tafiyar da harkokin mulki.


1 2 3