Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:31:14    
Bayani a kan Confucius

cri

Akwai wani karamin kundin littafin da ya shahara kwarai da gaske a kasar Sin. Littafin ya tsara ra'ayoyin Confucius da maganganunsa da kuma hirar da ya yi tare da almajiransa a ciki. A zamanin da a kasar Sin, littafin ya kasance mai matukar muhimmanci tamkar Good Bible a kasashen yammaci. Idan mutum talaka ne, to, dole ne ya kayyade zaman rayuwarsa bisa wannan kundin littafi, sa'an nan, idan mutum yana son zama jami'i, to, dole ne ya karanta wannan littafi sosai da sosai. Amma a hakika, wannan littafi ba wai littafi ne na koyarwa ba, a'a, shi littafi ne cike yake da hikima. A cikin littafin, maganganun Confucius sun shafi fannoni da dama, ciki har da karatu da kide-kide da yawon shakatawa da yin abokai da sauransu. Yanzu, maganganu da dama da ke cikin wannan littafi sun riga sun zama karin magana da Sinawa ke amfani da su a kalmominsu na yau da kullum.

To, domin amsa tambaya ta biyu da malam Musa Maikano ya yi mana, yanzu bari mu dan tabo magana a kan tarihin CCTV international na kasar Sin. CCTV international wata tasha ce ta gidan telebijin na kasar Sin wadda ke watsa shirye-shiryensa cikin harshen Turanci awa 24 ko wace rana. An kaddamar da tashar a watan satumba na shekarar 2000. CCTV International tana dukufa kan bayar da labarai ga masu kallonta ko ina a duniya, kuma tana mai da hankali na musamman a kan kasar Sin. Tare da kungiyarta ta kwararru manema labarai, CCTV International ta kasance gudummawar da Sin ta bai wa duniya a fannin samar da labarai.(Lubabatu)


1 2 3