Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:31:14    
Bayani a kan Confucius

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Musa Maikano, mai sauraronmu da ya fito daga jihar Katsina da ke tarayyar Nijeriya. Kwanan baya, a cikin wata wasikar da ya turo mana, ya ce, don Allah ina da tambayoyi guda biyu wadanda nike so ku amsa mini a filinku na amsoshin tambayoyinku. Tambayoyin su ne, don Allah, me ake nufi da Confucius, sai kuma tambaya ta biyu a wace shekara ce aka kafa shahararren gidan telebijin na kasar Sin, wato CCTV INTERNATIONAL? To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani a kan Confucius tare kuma da CCTV INTERNATIONAL.

Masu sauraro, a yayin da ake tabo magana a kan al'adun gargajiyar kasar Sin, akwai wani mutumin da ba a iya mancewa da shi ba, wannan shi ne Confucius. Confucius babban malami ne da ya fitar da shahararren hasashen Confucius. Yau da shekaru 2000 da suka wuce, hasashen Confucius yana bayar da tasirinsa a kan harkokin siyasa da al'adu da ma sauran fannoni daban daban na kasar Sin, bayan haka, yana kuma haifar da tasiri a kan halayyar Sinawa da kuma tunaninsu. Har ila yau wasu malaman kasashen waje sun dauki tunanin Confucius bisa matsayin tunanin addinin kasar Sin. Amma a hakikanin gaskiya, tunanin Confucius yana daya daga cikin hasashe da yawa na zamanin gargajiyar kasar Sin ne kawai, kuma shi wani irin tunanin filosofiya ne, amma ba wani irin addini ba ne. Bayan haka, ba ma kawai tunanin Confucius ya kawo babban tasiri a kan al'adun kasar Sin ba, kai hatta ma wasu kasashen Asiya sun sha tasirinsa.


1 2 3