Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:28:32    
Kasar Sin ta nuna babban fifiko a gun gasar wasan kwallon tebur na duniya da aka yi Zagreb

cri

Dadin dadawa, shugaba Adham Sharara na hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya ya yi hasashen cewa, kasashen Turai na baya-baya ne a fannin wasan kwallon tebur, in an kwatanta su da kasar Sin, kasar Sin ta sami irin wannan nasara ne ba domin taki sa'a ba. Kasar Sin ta nuna fifiko daga fannoni 3, wato kasar Sin tana dora muhimmanci kan wasan kwallon tebur, sabbin 'yan wasa su kan gaji fasahohi daga nagartattun magabatansu, sa'an nan kuma, 'yan wasa suna karawa da juna bisa matsayin koli a gida. Irin wadannan dalilai 3 da kasashen Turai ba su mallaka ba sun sanya kungiyar kasar Sin ta fi nuna karfi a duk duniya a yanzu, mai yiwuwa ne ta kwashe dukkan lambobin zinariya a cikin kananan gasanni 4 na wasan kwallon tebur a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa. Ya ce,'Su ne 'yan wasa mafi kyau a duniya, amma tilas ne mu san dalilin da ya sa hakan. A idona, 'yan wasan Sin sun fi mai da hankali kan samun horo, malaman horas da wasanni na kasar Sin sun fi nuna gwaninta, sa'an nan kuma, akwai nagartattun 'yan wasan da suke sa kaimi ga juna domin samun ci gaba a kasar Sin. Irin wadannan dalilai 3 sun sanya kasar Sin ta fi nuna karfi a duniya a yanzu.'(Tasallah)


1 2 3