Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:28:32    
Kasar Sin ta nuna babban fifiko a gun gasar wasan kwallon tebur na duniya da aka yi Zagreb

cri

A gun wannan muhimmiyar gasar wasan kwallon tebur da aka yi, 'yan wasan kasashen Turai sun koma baya, ba yadda suka yi ba, sai ganin 'yan wasan Sin sun ci nasara. A cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, a gun gasannin tsakanin maza, 'yan wasan kasashen Turai sun iya yin karawa da 'yan wasan kasar Sin domin zama zakara. Amma a gun gasar da aka yi a wannan karo, sun ci cikakkiyar tura, sun rasa damar shiga karon kusa da karshe na ko wace karamar gasa. Masu aikin wasan kwallon tebur na kasa da kasa suna ganin cewa, ko da yake 'yan wasan Turai sun taba zama manyan abokan gaba ga 'yan wasan Sin, amma a cikin shekaru misalin 10 da suka shige, ba su sabunta fasaharsu ba, ba su sami ci gaba ba, duk da haka, 'yan wasan Sin sun yi ta samun ci gaba a fannin sabunta fasaha. Don haka gibin da ke tsakanin 'yan wasan Turai da na Sin ya karu.

Dan wasa Li Jing na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, wanda ya sami lambar azurfa a cikin gasar tsakanin maza biyu biyu a gun taron wasannin Olympic na Athens, ya kuma shiga hadaddiyar gasar wasan kwallon tebur ta Turai, a bayyane ne ya nuna ra'ayinsa kan irin karuwar gibin da ke tsakanin 'yan wasan Sin da na Turai, ya ce,'Yanzu yawancin malaman horas da wasanni na kasashen Turai sun rike da tunani irin na shekaru 1990, ba su san ci gaban wasan kwallon tebur sosai ba, a ganinsu, fasahar da suke mallaka a da ta ishe su. Amma kungiyar kasar Sin ta riga ta samar da sabbin fasahohi, ban da wasu nagartattun 'yan wasan Turai maza kamar shi Boll Timo, dukkan sauran 'yan wasan Turai ba su mallaki irin wadannan fasahohi ba. Ina tsammanin cewa, nan da shekaru 10 har ma 20 masu zuwa, da kyar 'yan wasan Turai za su cim ma takwarorinsu na kasar Sin.'


1 2 3