Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:28:32    
Kasar Sin ta nuna babban fifiko a gun gasar wasan kwallon tebur na duniya da aka yi Zagreb

cri

An yi gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta duniya a karo na 49 a birnin Zagreb tun daga ran 21 zuwa na 27 na watan Mayu. 'Yan wasa daga wurare daban daban na duniya sun yi alla-alla wajen zama zakara. Amma a yayin da ake ci gaba da gasar, 'yan wasa da yawa sun yi bakin ciki saboda sun gano cewa, a yawancin lokaci sun bai wa 'yan wasan kasar Sin taimako ne kawai domin su zama zakaru a gun gasar. Sakamakon gasar kuwa ya shaida ra'ayoyinsu. A cikin karon karshe na gasa ta tsakanin namiji da namiji da ta tsakanin mace da mace da ta tsakanin maza biyu biyu da ta tsakanin mata biyu biyu da ta gaurayawar namiji da mace, 'yan wasan kasar Sin ne kawai suka yi takara da juna. 'Yan wasan Sin ba kawai sun kwashe dukkan lambobin zinariya a cikin wadannan gasanni 5 ba, har ma sun nuna babban karfinsu duka. Ko da yake kasar Sin ta dade da zama kan gaba a duniya a fannin wasan kwallon tebur, amma ba ta taba nuna irin wannan fifiko a gun gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta duniya a cikin shekaru misalin 20 da suka wuce ba. Shugaban kungiyar kasar Sin kuma mataimakin hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin kuma dan majalisar hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya Cai Zhenhua ya yi hasashen cewa,'Ma iya cewa, mun sami nasara mafi kyau a tarihi, mun kwashe dukkan lambobin zinariya da azurfa a cikin kananan gasanni 5, haka kuma 'yan wasanmu sun zama na uku a cikin kananan gasanni 4, muna cewa, kasar Sin ta shiga wani sabon zamanin zinariya.'


1 2 3