Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-31 19:54:24    
Jam'iyyun siyasa na demakuradiya da suke sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da kuka saba da sauraronsa na Me Ka Sani Game da Kasar Sin.A cikin wannann shirinmu na yau,za mu cigaba da yi muku bayani kan jam'iyyun siyasa na demakuradiya da suka sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin.

Jam'iyyar demakuradiya ta hudu da take taka rawa a cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce kungiyar bunkasa demakuradiya ta kasar Sin.An kafa wannan kungiyar ne a ran 30 ga watan Disamba na shekara ta 1945.lokacin da aka kafa wannan kungiya,yawancin 'yan kungiyar sun zo ne daga fannonin al'adu da ilimi da dabi da kuma 'yan kasuwa masu kishin kasa na demakuradiya na birnin Shanghai.

A cikin sabon kundin tsarin ka'idoji na kungiyar nan da aka zartas a taron wakilan kasa a karo na tara da aka yi a watan Disamba na shekara ta 2002,an tanadi cewa kungiyar nan tana tafiyar da harkokinta na yau da kullum bisa tsarin mulkin kasa na jamhuriyar jama'ar kasar Sin.Tsarin siyasa na kungiyar nan a matakin farko na zaman gurguzu shi ne bisa jagorancin akidar Deng Xiaoping,kungiyar ta yi nazari da aikata abubuwan da muhimmin tunanin "wakilci a fannoni uku" ya kunsa,ta kammala ayyukanta a kan matsayin jam'iyyar siyasa mai sa hannu cikin harkokin siyasa,ta kuma daga tutar masu kishin kasa da gurguzu sama,ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da babban tafarki na mai da ayyukan raya tattalin arzikin kasa tamkar cibiya da nacewa ga bin manyan ka'idoji guda hudu da kuma yin gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje,tana yin gwagwarmayar shimfida zaman jin dadi ga jama'a da mai da kasa ta zama ta zamani da kuma neman dinkuwar kasa da kiyaye zaman lafiya na duniya da gaggauta bunkasuwa tare da kuma mai da kasarmu ta zama kasar gurguzu mai wadata da demakuradiya da wayewar kai.

Har zuwa karshen shekara ta 2005,kungiyar bunkasa demakuradiya ta kasar Sin tana da sassa 302 a matakin yankuna da gundumomi a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye 29 da sauran sassan kasa 5806,yawan 'yan kungiyar ya kai dubu 99.

Jam'iyyar siyasa ta demakuradiya ta biyar dake taka rawa a cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce Jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin.Jam'iyyar nan ta kafu ne a watan Augusta na shekara ta 1930.Mutane masu ilimi mai zurfi ko matsakaici a fannin kiwon lafiya na kasar Sin ne ginshikan jam'iyyar.

Bayan da kasar Sin ta shiga cikin wani sabon mataki,jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta karkata hankalinta ga ba da hidima ga ayyukan mai da kasa zaman gurguzu na zamani,ta nuna kwazo da himma wajen shiga harkokin siyasa da sa ido ta hanyar demakuradiya,da bayar da ra'ayoyi da shawarwari ga ayyukan kawo sauyi da bunkasa tattalin arziki da al'adu da na kiwo lafiya,ta ba da taimakonta ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin wajen tabbatar da manufofin siyasa game da masu ilimi.'ya'yan Jam'iyyar su kan aza sawunsu a yankuna masu talauci da samarwa dabarun bunkasa tattalin arzikin yankunan da kawo shawarwari da bayar da ilimi bayan aiki da kuma bayar da taimako a fannin ilimi ga yankunan dake dab da iyakar kasa,jam'iyyar ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ayyukan kawo sauyi da bude kofa ga kasashen waje da inganta da bunkasa hadaddiyar kungiyar masu kishin kasa da kiyaye halin siyasa na kwanciyar hankali da hadin kai.

Jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin tana da sassanta a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye su talatin ban da Taiwan da Tibet,'ya'yan jam'iyyar sun kai fiye da dubu tamanin.

Jam'iyyar demakuradiya ta shida dake sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin.Jam'iyyar ta hada da manyan da daidaiku na sinnawan da suka dawo daga ketare da kuma iyalansu da kuma mutanen dake da alaka da kasashen ketare.

A watan Oktoba na shekara ta 1925 a birnin Los Angeles na Amurka ne wata kungiyar Zhigong ta sinnawan dake zama a latin Amurka ta kafa wannan jam'iyya.Cikin dogon lokaci jam'iyyar Zhigong ta yi gwagwarmaya domin neman mulkin kai da 'yancin kasa da kuma kare moriyar adalci ta sinawan da ke zama a kasashen ketare.A taron wakilan kasa a karo na uku da aka yi a watan Mayu na shekara ta 1947,jam'iyyar Zhigong ta yi garambawul,daga nan ta kama hanyar ba da sahihin hadin kai ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da yin gwagwarnmaya tare.Cikin bin manyan ka'idojin da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasa na Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin,jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin tana tafiyar da harkokinta cikin yanci.Jam'iyyar Kwaminis ta Sin jam'iyya ce dake tafiyar da harkokin mulkin kasa,jam'iyyar Zhigong ta ba cikakken hadin kai,tana dukufa kain da nain wajen bunkasa zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin.

Jam'iyyar demakuradiya ta bakwai da ke sa hannunta cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce jam'iyyar nazarin ilimi ta ran 3 ga watan Nuwanba.manyan masana da madaidaiku masu ilimi ne a fannin nazarin ilimin kimiyya da fasaha su ne gishinkan jam'iyyar nan,jam'iyyar ta karbi shugabancin jam'iyyar kwaminis ta Sin ta hada kanta sosai da Jam'iyyar kwaminis ta Sin tana kokarin gina zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin.

Asalin jam'iyyar ya zo ne daga wata kungiyar tattaunawa ilimin kimiyya na demakuradiya da wasu masana masu kishin kasa dake yin dagiya da mayaudara imperism a turance suka kafa a birnin Chongqing tare da nufin neman demakuradiya da kimiyya.Domin tunawa da babbar nasara da aka samu a cikin yakin kin harin Japan da yakin kin 'yan fasist na duniya a ran 3 ga watan Satumba na shekara ta 1945 aka canja sunan jam'iyyar zuwa jam'iyyar nazarin ilimi ta ran 3 ga watan Satumba,a hukunce aka kafa jam'iyyar a ran 4 ga watan Mayu na shekara ta 1946.Jam'iyyar tana da nata kwamiti ko kwamitin share fage a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya su talatin da sauran birane da gundumomi 268 ban da Taiwan da Tibet.'ya'yan jam'iyyar sun kai dubu 88,kashi 60 bisa dari masana ilimi mai zurfi ne.

Jam'iyyar demakuradiya ta takwas dake sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce kawancen mulkin kai na demakuradiya na Taiwan.A ran 12 ga watan Nuwanba na shekara ta 1947 a birnin Hongkong ne aka kafa shi wanda ya hada ma'aikata da masu kishin kasa da suka zo daga lardin Taiwan,jam'iyyar siyasa ce dake bautawa gurguzu,kawancen ya ba da cikakken hadin kai ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.An kaurar da hedkwatar kwamitin tsakiya na kawancen nan daga Taiwan daga Taiwan zuwa babban yankin kasar Sin a shekara ta 1949,da farko an kafa hedkwatar a birnin Shanghai,an kaurar da ita zuwa birnin Beijing a shekara ta 1955.

Jama'a masu sauraro,har zuwa yanzu mun gabatar muku da jam'iyyun siyasa guda takwas na demakuradiya da suke sa hannayensu cikin harkokin siyasa na kasar Sin.mun kwana a nan.(Ali)