Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 07:55:29    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (09/05-15/05)

cri

Ran 12 ga wata da dare,aka bude zama na 7 na taron wasannin nakasassu na kasar Sin a birnin Kunming dake kudancin kasar Sin.`Yan wasa nakasassu sun zo ne daga larduna da jihohi da birane 31 a duk fadin kasar Sin,ban da wannan kuma,wakilan `yan wasa nakasassu da suka zo daga rukunin gina Xinjiang da Hongkong da Macau su ma sun halarci wannan gagarumin taron wasanni.A gun wannan taro,gaba daya aka kafa wasannin gasa 20,kuma an riga an kammala biyar daga cikinsu.

Ran 13 ga wata,aka fara yin gasar cin kofin Asiya na wasan kwallon kafa cikin daki na shekarar 2007 a birnin Osaka da birnin Amagasaki na kasar Japan,za a yi kwanaki 7 ana yin gasar.A gun gasa ta farko,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Malaysia da 2 bisa 0,wato ta samu nasara ta farko,kungiyar kasar Japan kuwa ta lashe kungiyar kasar Philipines da 16 bisa 0.

Ran 13 ga wata,aka kammala budaddiyar gasar wasan kwallon badminton ta kasar Indonesia ta shekarar 2007,kungiyar kasar Sin ta samu lambawan sau uku,wato Fu Haifeng da Cai Yun sun zama zakarun gasa dake tsakanin maza biyu biyu,Du Jing da Yu Yang sun zama zakarun gasa dake tsakanin mata biyu biyu,ban da wannan kuma,Zheng Bo da Gao Ling sun zama zakarun gasar gaurayawar namiji da mace.

Ran 13 ga wata,aka kammala gasar cin kofin duniya ta wasan hoki kan kankara ta shekarar 2007 a birnin Moscow na kasar Rasha,kungiyar kasar Canada ta lashe kungiyar Finland da 4 bisa 2,wannan shi ne zakara ta 24 da kungiyar Canada ta zama a tarihin gasar cin kofin duniya.Kungiyar kasar Finland ta samu lambatu,kungiyar kasar Rasha ta lashe kungiyar kasar Sweden ta samu lambatiri.(Jamila Zhou)