Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-12 20:00:57    
Saukaken tarihi na Marigayi Mao Zedong

cri

An haifi marigayi shugaba Mao Zedong ne a gundumar Xiangtan ta lardin Hunan ta kasar Sin a ran 26 ga watan Disamba na shekara ta 1893,ya rasu a ran 9 ga watan Satumba na shekara ta 1976.Yana daya daga cikin manyan shugabannin kasar Sin wadanda suka kafa Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin da Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin.Shi kuma dan Marksanci ne mai girima da kuma dan juyin juya hali ne da masani shiri da hasashe na talakawa.Tun yana yaro,ya fara karatunsa a makaranta mai zama kansa.

Bayan da aka ta da bore a birnin Wuchang a shekara ta 1911,ya shiga wata sabuwar rundunar soja ta lardin Hunan.Tsakanin shekara ta 1914 da ta 1918 yana karatu a makarantar horaswar mallamai ta farko ta lardin Hunan da ke birnin Changsha.A watan Afril na shekara ta 1918 ya hada kansa da abokinsa Cai Hesheng da sauran abokansa ya kafa kungiyar nazarin ilmin sabon dimakuradiya,ya kintsa 'yan kungiyar da su fasahohin da aka samu a cikin juyin juya hali na watan Oktoba na kasar Rasha,ya kokarta wajen samo hanyoyi da dabaru na kawo wani canji a kasar Sin.A yanayin hunturu na wannan shekara ya zo birnin Beijing,ya zama wani ma'aikaci a cikin dakin ajiye littattafai na jami'ar Beijing wanda marigayi Li Dazhao shi ne darektansa.A ran 4 ga watan Mayu na shekara ta 1919,tare da kwazo da himma ya shiga wani zanga zanga da da 'yan makarantu na birnin Beijing suka yi,ya kuma shirya wata mujjala "Sharhin Xiangjiang" domin yin adawa da mayaudara da kuma mulkin gargajiya.Tun daga shekara ta 1921 bi da bi ya kafa kungiyar nazarin al'adu da kungiyar nazarin harkokin Rasha da kungiyar samari na zaman gurguzu da wata tawaga ta kwamsanci ta lardin Hunan.

A watan Yuli na shekara ta 1921 ya halarci taro na farko na wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na kasa baki daya.A watan Augusta ya zama darekatan reshen Hunan na ma'aikatar kula da kwadago ta kasar Sin,ya ba da jagora ga ma'aikata wajen tafiyar da harkokinsu.A shekara ta 1922 ya zama sakatare na kwamitin Hunan na jama'iyyar Kwaminis ta Sin.A watan Yuni na shekara ta 1923 ya halarci taro na uku na wakilan dukan saka na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,an kuma zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na kwamitin zartaswa na tsakiya da kuma manban ofishin kwamitin tsakiya da sakare.Bayan da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta hada kanta da jam'Iyyar Kuomintang ta kasar Sin,bi da bi ya halarci taron wakilan kasa baki daya na farko da na biyu na Jam'iyyar Kuomintang,aka zabe shi mamba ba cikakke ba na kwamitin zartaswa na tsakiya.

A shekara ta 1925 ya zama mukkadashin shugaba na ma'aikatar fadakar da jama'a ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kuomintang,ya kuma shirya wata" jaridar mako-mako ta siyasa" wadda ita ce mujjalar hukuma ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kuomintang.A shekara ta 1926 ya kafa wata makarantar horar da manoma a karo na shida,ya horar da manoma ginshikai wajen tafiyar da harkokinsu.A watan Nuwanba na wannan shekara ya zama sakatare na kwamitin kula da harkokin manoma na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.A watan Afril na shekara ta 1927,ya halarci taron wakilan kasa baki daya a karo na biyar na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,aka zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na kwamitin tsakiya,a watan Yuni ya zama sakatare na kwamitin Hunan na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

A gun taron ran bakwi ga watan Augusta na wannan shekara na Jam'iyyar ya gabatar da wani shahararren ra'ayinsa wato "daga bakin bindiga ake samun mulkin kasa",aka zabe shi da ya zama mamba ba cikakke ba na ofishin siyasa na wucin gadi na kwamitin tsakiya.Bayan taron ya ta da tawaye na yanayin kaka a yankunan dab da iyaka da ke tsakanin lardin Hunan da lardin Jiangxi,daga baya ya ja ragamar rukunin masu bore zuwa yankin tsaunuka na Jinggangshan ya kafa sansanin juyin juya hali na kauyuka na farko.A shekara ta 1928,rukuninsa ya hada da rukunan masu bore da marigayi Zhu De da Chen Yi ke jagora,aka kafa rukuni na hudu na rundunar soja ta juyin juya hali na ma'aikata da manoma( ba da dadewa ba aka canza sunanta zuwa jar rundunar soja),ya zama wakilin Jam'iyyar kuma sakatare na kwamitin fagen daga.

Tare da idon basira 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin wadanda marigayi Mao Zedong muhimmin wakilinta sun bude wata hanyar juyin juya hali na samun mulkin kasa da makami ta dabarar yi wa birane zobe daga kauyuka da kuma kwace birane daga bisani bisa halin da kasar Sin ke ciki a wannan lokaci.A shekara ta 1930 ya zama babban kwamishinan siyasa na rukunin farko na jar runduna soja.A shekara ta 1931,ya zama shugaban gwamnatin tsakiya ta rikon kwarya ta Jamhuriyar Soviet ta kasar Sin.A watan Janairu na shekara ta 1933 aka zabe shi da ya zama dan ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin.Tun daga karshen shekara ta 1930,Shi kansa da mallam Zhu De sun ja ragamar rukunin farko na jar rundunar soja wajen murkushe "zobe" na karo na farko da na biyu da na uku da sojojin Jam'iyyar Kuomintang.Duk da haka aka tilasta shi da ya bar guraban shugabanci na jam'iyyar da rundunar soja bisa matsin lamba da masu tsatsaurn ra'ayi na jam'iyyar suka yi masa.A watan Oktoba na shekara ta 1934,rukunin farko na jar rundunar soja ya fara doguwar tafiya wato long march a turance bayan da ya sha hassara a cikin "zobe" a karo na biyar da aka yi masa.A hanyar doguwaar tafiya a gun taron Zongyi da aka yi a watan Janairu na shekara ta 1935,aka gyara kuskuren da masu tsatsauran ra'ayi na jam'iyyar suka yi aka tabbatar da matsayin shugabanci na marigayi Mao Zedong a cikin jam'iyyar kwaminis ta Sin da rundunar soja.

Bayan daJar rundunar soja ta isa arewancin lardin Shanxi tare da nasara,a watan Disamba na shekara ta 1935,marigayi shugaba Mao Zedong ya bayar da wani rahoto kan dabarun yaki da mahara japannawa,a cikin rahotonsa ya gabatar da wata manufar kafa hadaddiyar kungiyar adawa da mahara Japannawa ta al'umma.Bayan da yakin adawa da mahara Japannawa ya barke a shekara ta 1937,kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wanda marigayi shugaba Mao ke wakilinsa ya nace ga bin ka'idar 'yancin kai cikin hadaddiyar kungiyar yin adawa da mahara Japannawa,ya yi kokarin ta da mutanen Sin da su yi yakin sari-ka noke bayan fagen yaki,ya kafa sansanoni da dama na yin adawa da mahara Japannawa da neman dimakuradiya.A watan Maris na shekara ta 1943,aka zabi marigayi Mao Zedong da ya zama shugaban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.A gun taron wakilan kasa baki daya a karo na bakwai na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka yi a shekara ta 1945,aka mai da tunanin Mao Zedong ya zama tunanin jagora ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.Daga cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na bakwai na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,yana kan kujerar shugaban kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin har zuwa rasuwarsa.Bayan yakin adawa da mahara Japannawa ya sami nasara,a watan Augusta na shekara ta 1945,Shi kansa ya je birnin Chongqing don tattaunawa,ya yi iyakar kokarinsa wajen neman zaman lafiya da shimfida dimakuradiya.A yanayin rani na shekara ta 1946,Jiang jeshi ya tayar da yakin basasa daga dukkan fannoni,marigayi shugaba Mao da sauran shugabanni na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun yi jagora a cikin babban yakin suncin jama'a,a shekara ta 1949,aka hamburar da mulki na Jam'iyyar Kuomintang.

A gun cikakken zama na farko na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar Kasar Sin da aka yi a watan Satumba na shekara ta 1949,marigayi Mao Zedong ya ci zaben zama shugaban gwamnatin jama'a ta tsakiya ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.A lokacin farko na kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin,shi kansa da sauran shugabanni na kwmitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun ja ragamar jama'ar kasa wajen komada tattalin arzikin kasa da gyara tsarin mallakar gonakai tare da nasara,sun kuma danne wadanda suka yi adawa da juyin juya hali,sun tura sojoji masu sa kai zuwa Korea domin yin adawa da Amurka da ba da tallafi ga Korea,ban da wannan kuma sun yi kokarin inganta mulkin kasa da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali.A karshen shekara ta 1952,ya gabatar da wani babban tafarki ga jam'iyyar a lokacin rikon kwarya,ya kuma tsara ka'idoji da manufofi a jere domin kakkafa masana'antu na zaman gurguzu,gwamnati ta kawo canji ga ayyukan aikin gona da sana'ar hannu da kuma ayyukan masana'antu da ciniki na masu jarin hujja bisa hanyar zaman gurguzu.A Shekara ta 1954,ya ba da jagora wajen tsara kundin tsarin mulkin kasa na farko,kuma aka zabe shi da ya zama shugaban Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin a gun taron wakilan jama'ar kasa baki daya na farko.

A watan Fabrairu na shekara ta 1952,ya bayar da wani jawabi "kan daidaita matsaloli dangane da sabani tsakanin jama'a yadda ya kamata",ya ba da ra'ayinsa a kan cewa kamata ya yi a bambanta sabanin dake tsakanin jama'a da sabanin dake tsakanin jama'a da abokan gaba,ya maida daidaita sabanin dake tsakanin jama'a cikin ajandar harkokin siyasa na gwamnatin.A shekara ta 1958,ba tare da dogon tunani ba ya yi yunkurin neman samun cigaba fiye da kima,da kuma kakkafa kungiyoyin noma na jama'a a kauyuka.A shekara ta 1966,ya aikata kuskuren ta da "juyin juya hali na al'adu",wannan ya kawo mummunan barna da hassara ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatinta a fannoni da yawa.

A shekarun saba'in na karni da ya shige,ya bayar da ra'ayi na shata duniya gidaje uku wato Amurka da Rasha suna cikin gida na farko da sauran kasashe masu cigaban masana'antu suna cikin gida na biyu da kasashe matasa suna cikin gida na uku.Ya juya dangantaka dake tsakanin kasar Sin da Amurka,daga nan wani hali mai armashi ya bullo a harkokin waje na kasar Sin.A ran 9 ga watan Satumba na shekara ta 1976,mallam Mao Zedong ya rasu a birnin Beijing.Da ya ke marigayi shugaba Mao Zedong ya yi kuskure a karshen rayuwarsa,taimakon da ya baiwa juyin juya hali na kasar Sin ya fi yawa,kuma dauwamame ne,shi ne babban jagora na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da na mutanen kabilu dabam daban na kasar Sin.Tunanin Mao Zedong da aka samu a cikin yunkurin da Jam'iyyar da mutanen Sin suka yi tare,dukiya ce mafi daraja ga Jam'iyyar kuma tunanin jagora ne ga Jam'iyyar.