Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-04 14:08:28    
An soma taron shugabannin kasashen kudancin nahiyar Asiya

cri

A ran 3 ga wata an soma taron shugabannin kungiyar hada kan kasashen kudancin nahiyar Asiya na 14 a birnin New Delhi, babban birnin kasar Indiya. Shugabannin kasashen kungiyar da wakilan kasashe 5 ciki har da kasar Sin wadanda suke kan matsayin 'yan kallo sun halarci bikin kaddamar da taron. Wannan ne taron shugabanni na farko da kungiyar ta yi bayan da ta tsai da kudurin shigar da sabbin membobi da kasashe 'yan kallo.

A gun wannan taro, shugabanni za su tattauna kan batutuwan fama da talauci da cinikayya da ilmi da fama da ta'addanci da dai makamatansu tare da kuma za a zartas da sanarwar da abin ya shafa. A cikin nasa jawabin da ya yi a gun bikin kaddamar da taron, Mr. Manmohan Singh, firayin ministan kasar Indiya, mai shirya taron, ya taya kasar Afghanistan murna domin ta zama memba ta takwas ta kungiyar. Ya kuma yi marhabi da wakilan kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu da Amurka da kungiyar Turai da suke halartar taron a matsayin 'yan kallo. Ya ce, "Ina farin ciki sosai saboda manyan wakilan kasashe da ba na yankinmu ba su halarci taronmu a matsayin 'yan kallo. Nan da shekaru masu zuwa, kungiyar hada kan kasashen kudancin nahiyar Asiya za ta kara yin hadin guiwa da kasashe abokanmu da ba na cikin yankinmu ba domin shigarsu a cikin ayyukan raya yankinmu."

Mr. Singh ya kara da cewa, yanzu kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya tana cikin halin yin gyare-gyare kan harkokin siyasa da tattalin arziki da ba a taba gani ba a da. Za a ji zafi a cikin wannan halin da ake ciki. Sabo da haka, ana fatan kowace membar kungiyar za ta yi kokarinta, gwamantocin kasashe daban-daban ma "za su iya yin watsi da sabane-sabanen da ke kasancewa a tsakaninsu domin hada kan juna wajen neman cigaba."

A cikin nasa jawabi, Mr. Shaukat Aziz, firayin ministan kasar Pakistan ya ce, ko da yake kasashen kudancin Asiya sun samu wasu cigaba, amma suna da bayayyen karfin da za a iya amfani da shi. A gaban duniyar da take samun sauyi cikin sauri, dole ne kasashen kudancin Asiya su fuskanci halin da suke ciki da yin nazari kan halin da suke ciki, kuma su daina yin muhawarar da ake yi ta yi, sai su dauki hakikanan matakan neman cigaba. Mr. Aziz ya ce, "Dukkanmu muna dukufa kan ayyukan raya kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya. Dole ne mu sa niyya da yin amfani da hankalinmu da karfinmu mu canja kudancin nahiyar Asiya domin yankinmu ya zama wani yankin da ke da karfi da cigaba da bunkasuwa tare. Wannan nauyi daya ne da ke bisa wuyanmu. Dole ne mu canja tunani da matsayin da muke dauka domin cimma wannan buri."

Mr. Hamid Karzai, shugaban kasar Afghanistan wanda ya halarci taron shugabannin kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya a karo na farko ya bayyana cewa, bayan da aka shigar kasar Afghanistan a cikin kungiyar, bangarorin biyu za su iya moriyar juna. Da farko dai, za a iya kawo karshen halin ware da kasar Afghanista ta dade take ciki, kuma za ta iya samun cigaba a karkashin taimakawar kasashen kudancin Asiya. Sannan kuma sauran kasashen kungiyar za su iya samun moriya daga ayyukan sake raya kasar Afghanistan. Mr. Karzai ya ce, "Kasar Afghanistan ta zama membar kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya a hukunce, wannan ya zama wata dama mai kyau ga yunurin sa kaimi wajen yin cudanya a tsakanin jama'ar yanki da kara samun moriyar tattalin arziki ga yankinmu. Sabo da haka, mun sanya manufar kara yin hadin guiwa a yankin a cikin manufofin da suke gaban kome. Ya kuma zama babban shirin da kasar Afghanistan take bi wajen neman bunkasuwa."

A gun bikin kaddamar da taron, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya wakilci gwamnatin kasar Sin ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, "Gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya wajen cimma burinsu da neman bunkasuwa a wasu fannoni. Kasar Sin tana son yin hadin guiwa mai hakikanci da kasashen kungiyar bisa ka'idojin girmama burin kasashen kungiyar da zaman tare cikin lumana domin shimfida zaman lafiya da cigaba a yankin kudancin Asiya har a duk duniya."

Mr. Li ya kuma bayar da hakikanan matakai yadda za a kara yin hadin guiwa da kasashen kungiyar hada kan kasashen kudancin Asiya. (Sanusi Chen)