Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-22 20:25:49    
Bayyanin kan Shirin shekaru 5-5 na raya kasa na 10 na Lardin Heilongjiang(B)

cri

A wajen samar da wutar lantarki , wurare daban daban na kasar Sin suna bin wata manufar cewa , da farko dai za a samar da wutar lantarki ga zaman yau da kullum na jama'a.

Jin Ziyang , mataimakin babban manajan Kamfanin samar da wutar lantarki na Lardin Heilongjiang ya bayyana cewa , don kasa kayyade amfanin wutar lantarki da tabbatar da aikin samar da wutar lantarki ga farar hula , a wannan shekara mun yi aikin musamman don kula da bukatar jama'a . Mun tsara wani shirin wanda ya jibinci masana'antu fiye da dubu 30 .

Jama'a masu sauraro , abin da kuka saurara dazu nan shi ne labarin kasa kan Lardin Liaoning . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan makamashin Lardin . Kwanan baya gwamnatin Liaoning ta kira taron aiki kan yadda za a yi tsimin makamashi . Qian Yunlu , sakataren Kwamitin Heilongjiang na jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin da Zhang Zuoyi , shugaban Lardin Heilongjiang sun yi jawabi daya bayan daya kan aikin tsimin makamashi . Mr. Zhang ya jaddada cewa , za mu yi kokari don mai da lardin Heilongjiang da ya zama lardi mai tsimin makamashi kuma yana kasancewa da muhalli mai kyau da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci .

Zhang Zuoyi , Shugaban Lardin Heilongjiang da mataimakinsa su kuma sun yi jawabi , inda suka bayyana cewa , A ran 2 ga watan Satumba a nan birnin Harbin , An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar Lardin . Taron ya zartas da Shirye-shiryen raya tattalin arzikin birnin da zaman al'umman Lardin Heilongjiang a shekaru 5 masu zuwa da rahoton aikin gwamnatin Lardin.

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin Lardin na shekara-shekara zai kai kashi 9 cikin 100 . Kuma an tabbatar da manufar rage yawan makamashin da za a yi amfani da rage yawan gurbatattun abubuwan da za a fitar . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kafa sababbin kauyyuka da hanzarta gyare-gyaren tattalin arziki da ciyar da Bunkasuwar birane da gundumomi cikin daidaici , za su zama tsarin musamman na manyan ayyukan Lardin .

Mr. Zhang , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta lardin HeiLongjiang Ya yi nuni da cewa , a wajen kiyaye ikon musamman na lambobin kasuwanci da aka yiwa rajista , Lardin Heilongjiang tana mai da hankali sosai kan lambobin kasuwanci na kasar Sin da na kasashen waje .

Ya kuma bayyana cewa , a cikin shekaru 5 da suka shige , mun dauki aikin kiyaye shahararrun lambobin kasuwanci na kasashen waje kamar wani muhimmin aiki na Lardin . Musamman ma daga shekarar 2004 zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara , Ofishin lura da lambobin kasuwanci da Kwamitin duba lambobin na hukumar sun amince da shahararrun lambobin kasuwanci guda 30 na kasashen waje .

Kasar Sin tana daya daga cikin kasashe masu fama da lambobin jebu a duniya . Bayan da aka shiga sabon karni , kasar Sin ta dauki matakan magance laifufkan 'kera lambobin jebu .

A gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 15 ga wata a nan birnin Beijing , Li tong, shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta Lardin ya ce , kasar Sin ta yi na'am da wadannan shahararrun lambobin kasuwanci kuma tana kiyaye ikon mallakar ilminsu , ta sami yabo sosai daga masana'antu masu yawa musamman ma wasu manyan kamfanonin ketare kuma sun karfafa amincewar aikin kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasar Sin . Saboda haka , kasar Sin ta jawo hankulan kasashe masu yawa su zo nan kasar Sin don yin rajistar lambobinsu . Mu ma haka , Lardin Liaoning zai aiwatar da manufar gwamnatin kasar Sin , kuma za mu mai da hankali sosai kan kananan fannoni.(Ado)