Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 00:38:46    
Hu Jintao ya gana da Sam Nujoma

cri

A ran 6 ga wata a birnin Windhok, fadar kasar Namibiya, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da Sam Nujoma, wato tsohon shugaban kasar Namibiya ne da ya kafa kasar Namibiya,shugaban jam'iyyar kungiyoyin jama'a ta kudu maso yammacin Afirka, wato jam'iyyar SWAPO inda bangarorin biyu suka tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Namibiya da kuma a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Hu Jintao ya ce, lokacin da jama'ar kasar Namibiya suke yin gwagwarmayar neman 'yancin al'ummomin Namibiya, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi kokarin samar wa jam'iyyar SWAPO taimako. Bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Namibiya, jam'iyyun biyu wadanda yanzu suke kan mukamin mulkin kasarsu duka sun kara mai da hankali sosai wajen yin hadin guiwa a tsakaninsu a fannoni daban-daban, sun kuma sami sakamako da yawa. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son hada kan jam'iyyar SWAPO domin yin kokari tare wajen ciyar da zumunci da hadin guiwa da ke tsakaninsu gaba a kai a kai.

A cikin nasa jawabin, Mr. Sam Nujoma ya ce, jam'iyyar SWAPO tana kokarin kara ciyar da dangantakar sada zumunta da take kasancewa a tsakaninta da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da a tsakanin kasashen biyu gaba. Gwamnatin Namibiya da jam'iyyar SWAPO suna fatan za su iya kara yin hadin guiwar moriyar juna a tsakaninsu da kasar Sin a fannonin cinikayya da zuba jari domin kawo wa jama'arsu fatan alheri. (Sanusi Chen)