Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 21:33:16    
Kafofin watsa labaru cikin Sinnanci na kasar Afirka ta kudu suna mai da hankali sosai a kan ziyarar Hu Jintao

cri

A 'yan kwanakin baya, kafofin watsa labaru cikin Sinnanci na kasar Afirka ta kudu sun bayar da labarai da bayanai da yawa a kan ziyarar da shugaban kasar Sin Hu Jintao yake yi a kasar, ta wasu jaridu ne, bangaren Sinawa da ke Afirka ta kudu su ma sun bayar da bayanai a cikin jaridu da mujalloli don yin kyakkyawar maraba da ziyarar shugaba Hu a kasar.

A ran 6 ga wata, jaridar 'Africa Times' ta bayyana cewa, ziyarar da shugaba Hu yake yi zuwa kasashe 8 na Afirka ta zama wani mataki da kasar Sin ta dauka wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka daddale bisa tushen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, sabo da haka, wanna ziyara ta zama wata kyakkyawar damar kara sada zumunci a tsakaninsu.

Jaridar 'Sinawa ta Afirka ta kudu' ta bayar da wani bayanin edita a ran 5 ga wata, inda ta musunta maganar da aka yi wai kasar Sin tana gudanar da sabon salon mulkin mallaka a Afirka, lallai ba haka ba ne, kasar Sin tana ba da taimako ga Afirka ba tare da son kai ba, kuma suna cinikayya da juna cikin daidaici.(Danladi)