Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-06 08:35:38    
Shugaba Hu Jintao da takwaransa na Namibia sun yi shawarwari

cri

Ran 5 ga wata, a birnin Windhoek, hedkwatar kasar Namibia, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ke ziyara a wannan kasa ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Namibia Hifikepunye Pohamba. Bangarorin 2 sun yarda da yin kokari tare wajen aiwatar da ra'ayi daya da suka samu don raya huldar aminci da hadin gwiwa da ke tsakaninsu zuwa sabon mataki.

A gun shawarwarin da aka yi, shugaba Hu ya bayyana cewa, yau da shekaru 17 da kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Namibia, manyan jami'ansu sun yi ta yin cudanya a tsakaninsu, kasashen 2 sun sami sakamako da yawa daga wajen hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki, sun kuma taimaka wa juna sosai a cikin al'amuran duniya. Kasashen Sin da Namiba abokai da kuma aminai ne da ke amincewa da juna. Ya kara da cewa, gwamnatin Sin tana gaggauta aiwatar da matakai da manufofi 8 da ta gabatar don karfafa hada kai a tsakaninta da Afirka da kuma goyon bayan bunkasuwar kasashen Afirka a gun taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, ta haka za a kara bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Namibia, da kuma tsakanin Sin da Afirka. Sa'an nan kuma, shugaba Hu ya ba da shawarwari 4 kan raya huldar da ke tsakanin kasarsa da kasar Namibia.

A nasa bangaren kuma, Mr. Pohamba ya ce, kasarsa na darajanta zumuncin da ke tsakaninta da kasar Sin, tana himmantuwa kan habaka da zurfafa hadin gwiwa domin moriyar juna a tsakaninta da kasar Sin a fannoni daban daban. Ya kara da cewa, ziyarar da shugaba Hu yake yi a wannan karo ta nuna cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakaninta da kasar Namibia, tana cika alkawarin da ta yi a gun taron koli na Beijing. Ya kuma amince da shawarwarin da shugaban Hu ya gabatar a fannin karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Namibia a fannoni daban daban.(Tasallah)