Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-05 21:42:06    
Shugaban kasar Sin ya fara yin ziyarar aiki a Nambia

cri

Bisa gayyatar da takwaransa na Nambia, Mr.Hifikepunye Pohamba ya yi masa ne, yau shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya isa birnin Windhoek, babban birnin kasar Nambia, don yin ziyarar aiki a kasar.

Bayan da shugaban kasar Sin ya isa filin jirgin sama, ya bayar da jawabi a rubuce, inda ya ce, Nambia tana daga cikin kasashen Afirka da suka sami 'yancin kansu a baya baya. A cikin shekaru 17 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da Sin, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi ta bunkasa lami lafiya, kuma bangarorin biyu sun sami manyan nasarori wajen hadin gwiwarsu a fuskokin siyasa da tattalin arziki da ilmantarwa da dai sauransu. Sin tana son yin kokari tare da bangaren Nambia, don bude wani sabon shafi kan hadin gwiwar aminci da ke tsakaninsu.

Shugaba Hu Jintao ya isa Nambia ne bayan da ya kawo karshen ziyararsa a kasar Zambia. A lokacin da yake ziyara a kasar Zambia, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Zambia. Mr.Levy Mwanawasa, sa'an nan ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar, Amusaa k. Mwanamwambwa, da kuma tsohon shugaban kasar, Kenneth David Kaunda. Bayan haka, kasashen biyu sun kuma bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi shelar kara inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban. (Lubabatu)