Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 16:48:05    
Waiwayen manyan lamura guda goma na shekarar 2006 game da aikin share faga ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Aminai makaunata, kuna sane da, cewa a shekarar 2006 da ta gabata ba da dadewa ba, ayyukan share fage ga taron wasannin Olympic da kuma taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a shekarar 2008 sun samu nasarori masu faranta ran mutane kwarai da gaske. To, a albarkacin zuwan sabuwar shekara, bari mu yi waiwayen manyan al'amura guda 10 da suka wakana a shekarar bara a duk tsawon lokacin da ake tafiyar da aikin share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing.

Muhimmin lamari na farko, shi ne an tabbatar da sunayen masu aikin yin fasalin bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 da kua bikin rufe shi. A ran 16 ga watan Afrilu, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya shelanta sunayen mambobin kungiyoyin yin fasalin bukukuwan nan guda biyu. Mr. Zhang yimou, shahararren mai ba da jagoranci ga nuna wasannin fasaha ya zama babban mai ba da jaroranci ga gudanar da wadanann bukukuwa guda biyu.

Muhimmin lamari na biyu, shi ne a ran 7 ga watan Agusta, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da zane-zanen alamanta wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Yawan zane-zanen ya kai 35, wadanda suka hada da wasan guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan tseren kananan jiragen ruwa, da wasan badminton, da wasan kwallon kwando, da wasan kwallon gora da kuma wasan dambe da dai sauransu.

Muhimmin lamari na uku, shi ne ran 8 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru biyu da suka rage ga gudanar da bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Mazauna birnin Beijing da na sauran birane da ke daukar nauyin shirya wasu gasanni na taron wasannin Olympic sun sha yin shagulgula a wannan rana. Shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing wato Mr. Liu Qi ya yi jawabin, cewa lallai ayyukan share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing da ake yi sun gamsar da mutane kwarai da gaske.

Muhimmin lamari na hudu, shi ne an soma yin gasannin jarrabawa domin taron wasannin Olympic na Beijing. A ran 20 ga watan Agusta, an yi gasar tseren kwale-kwale tsakanin kasa da kasa ta Qingdao a shekarar 2006 a cibiyar kwale-kwale ta Olympic ta Qingdao, inda za a gudanar da gasar tseren kwale-kwale ta taron wasannin Olympic na Beijing. Wannan dai wata gasar jarrabawa ce ta farko da aka yi domin taron wasannin Olympic na Beijing. Ban da wannan kuma, a ran 27 ga watan Agusta, an yi gasar jarrabawa daban, wato gasa ta 11 ta cin kofin duniya ta wasan kwallon softball na mata a unguwar Fengtai ta birnin Beijing.

Muhimmin lamari na biyar, shi ne da gaske ne aka gudanar da aikin daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic da kuma taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a shekarar 2008. Ana bukatar masu aikin sa kai da yawansu ya kai 70,000 domin taron wasannin Olympic na Beijing da kuma 30,000 domin taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.

Muhimmin lamari na shida, shi ne a ran 6 ga watan Satumba , wato daidai a ranar cika shekaru biyu da suka yi saura ga gudanar da bikin bude taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a shekararar 2008, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da abubuwan fatan alheri na taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a shekarar 2008.

Muhimmin lamari na bakwai, shi ne an shiga sabon matakin aikin gina babban dakin wasannin motsa jiki mai siffar ' Gidan tsuntsu' wato ' Bird's nest' a Turance na kasar Sin.

Muhimmin lamari na tawas, shi ne an tabbatar da shirye-shiryen ajandar taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Kwamitin zartaswa na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya rigaya ya amince da wannan ajanda.

Muhimmin lamari na tara, shi ne an bayar da farashin tikitocin kallon wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Bisa yanayin samun kudin shiga na jama'ar kasar Sin, an tabbatar da cewa, farashin tikitocin ya ragu kadan idan an kwatanta shi da na tarurrukan wasannin Olympic da aka yi a da. Za a soma sayar da tikitocin kallon wasannin Olympic na Beijig ne a farkon rabin wannan shekara.

Muhimmin lamari na goma wato na karshe, shi ne a ran 17 ga watan Disamba, a nan birnin Beijing, aka soma gudanar da yunkurin " Hadin gwiwa na zuriya da zuriya" domin ba da ilmi game da wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. ( Sani Wang )