Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 16:42:43    
Kasar Sin tana yin duk abubuwa da take iya yi wajen samar da ayyukan yi masu yawa

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, 'yan kwadago da suka yi rara a kauyuka sun kan yi kwarara zuwa garuruwa da birane don neman samun aikin yi. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan 'yan kwadagon nan ya wuce miliyan 125 a shekarar 2005, wato ke nan ya karu da miliyan 7 da dubu 550 bisa na shekarar 2004.

Malam Yin Jiankun, wani jami'in ma'aikatar jin dadin 'yan kwadago da zaman jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta taba tsara shirin ayyukanta da abin ya shafa don daga matsayin kwararewar wadannan 'yan kwadago. Ya kara da cewa, "tun daga shekarar bara, muka fara aiwatar da shirin nan. Bisa shirin, yawan 'yan kwadagon da za mu horar da su zai kai miliyan 40 a tsakanin shekarar 2006 zuwa ta 2010, wato ke nan za mu horar da su da yawansu zai kai miliyan 8 a ko wace shekara, ta yadda za mu daga matsayin kwarewarsu a fannin sana'o'i daban daban."

Bayan haka Malam Yin Jiankun ya kara da cewa, yanzu gwamnatin kasar Sin tana tsara wani shiri na kara samar da guraben aikin yi masu yawa har cikin wani dogon lokaci. Ya ci gaba da cewa, "da farko, yayin da muke kara bunkasa harkokin tattalin arziki, wajibi ne, mu kara samar da guraben aikin yi yadda ya kamata. Sa'an nan kuma ta hanyar da kara samar da guraben aikin yi masu yawa, za mu kara sa kaimi ga bunkasuwar harkokin tattalin arziki. Na biyu, ya kamata, a bar 'yan kwadago da su zabi ayyukansu da ake bukata a kasuwanni, hukumomin gwamnatin kuma za su sa kaimi ga kara samar da guraben aikin yi masu yawa. Na uku, ya kamata, a kyautata tsarin ba da tallafi ga masu neman aikin yi, ta yadda za a ba da tallafi ga 'yan kwadago na birane da kauyuka ba tare da biyan ko kwabo ba."

Ban da wadannan kuma, kasar Sin za ta kafa tsarin horar da duk 'yan kwadago a fannin sana'o'i daban daban, za ta gaggauta kafa kasuwannin samar da aikin yi, sa'an nan za ta kara kyautata tsarin ba da taimako ga wadanda aka sallame su daga aiki, da samar da ayyukan yi ga wadanda ke fama da talauci. (Halilu)


1 2