Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 16:42:43    
Kasar Sin tana yin duk abubuwa da take iya yi wajen samar da ayyukan yi masu yawa

cri

Kasar Sin tana da mutanenta da yawansu ya wuce biliyan 1.3, ta zama kasa mafi yawan mutane a duniya. Don haka samar da ayyukan yi wata dawainiya ce mai matukar wahala. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen kara samar da ayyukan yi masu yawa, kuma ta dauke su bisa matsayin babban aiki da take yi don daidaita matsalolin zaman rayuwar jama'a. Bisa kokarin da take yi, matane marasa aikin yi su kan yi kadan a kasar Sin.

Wata daliba mai suna Li Muhan wadda ke karatu a aji na hudu na Jami'ar Koyon Harsuna ta Beijing, ko da yake da sauran lokaci kafin ta gama karatunta daga jami'ar, amma ta riga ta fara yunkurin neman aikin yi. Da ta tabo magana a kan wannan, sai ta bayyana cewa, "a da mu kan nemi kamfanoni da muke sha'awarsu ta hanyar tasoshin Internet na hukumomin gwamnati daban daban, mu kan bata lokaci mai yawa. Amma yanzu muna yin haka ta hanyar tashar Internet da aka kafa cikin hadin guiwa musamman domin samar da ayyukan yi ga dalibai da za su gama karantunsu daga jami'o'i, lalle muna yinsa cikin sauki kwarai. "

Hukumar kula da harkokin raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin da ma'aikatar ilmi da ma'aikatar jin dadin 'yan kwadago da zaman jama'a da kuma sauran ma'aikatu biyu na kasar ne suka kafa wannan tashar Internet cikin hadin guiwarsu. A shekarar nan dalibai da za su gama karantunsu daga jama'o'i za su kai miliyan 4.9 a kasar Sin, wato ke nan ya karu sama da dubu 700 bisa na shekarar bara, amma yanzu kasar Sin ta riga ta dauki matakai a jere don samar musu da ayyukan yi.

1 2