Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 09:31:48    
(Sabunta)Hu Jintao ya yi shawarwari da Ellen Johnson-Sirleaf

cri

A ran 1 ga wata a birnin Monrovia, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf, gaba daya ne bangarorin biyu suka yarda da yin kokari tare domin ciyar da dangantakarsu ta abokantaka da juna da hadin kai gaba har ta kai wani sabon mataki.

Mr Hu ya ce, tun bayan da kasashen biyu suka maido da dangantakar diplomasiyya a shekarar 2003, shugabanninsu sun kara kai wa juna ziyara, kuma sun kara amincewa juna a fannin siyasa, haka kuma sun kara hadin kansu a fannonin tattalin arizki da cinikayya da ilmi da kiwon lafiya da al'adu da dai sauransu, kuma sun riga sun samu nasarori da yawa, ban da wannan kuma, bangarorin biyu su kan yi shawarwari da hada kai a kan harkokin duniya. Mr Hu ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Liberia wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da suka daddale da kara ciyar da dangantakarsu gaba.

Ellen Johnson-Sirleaf ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasar Liberia a fannoni daban daban, kasarta tana godiya sosai a kan haka, haka kuma kasar Liberia tana zura ido a kan kara hadin kai da kasar Sin a fannoin cinikayya da zuba jari da manyan ayyuka da dai sauransu.

Bayan shawarwarin da suka yi, Hu Jintao da Ellen Johnson-Sirleaf sun halarci bikin daddale yarjejeniyoyi 7 a tsakaninsu a kan fasahar tattalin arziki da kiwon lafiya da ilmi da aikin gona da dai sauransu. Ban da wannan kuma, Hu Jintao da Ellen Johnson-Sirleaf sun halarci cibiyar shawo kan zazzabin cizon sauro da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa.

A ran nan kuma, kasashen biyu sun bayar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa, inda suka yarda da kara hadin kai a fannoni daban daban da kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu.

A ran nan kuma, bayan da ya gama ziyararsa a kasar Liberia, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Monrovia, domin kai ziyara a kasar Sudan.(Danladi)