Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-02 09:04:24    
Hu Jintao ya kawo karshen ziyararsa a Liberia

cri

A ran 1 ga wata, bayan da ya gama ziyararsa a kasar Liberia cikin gajeren lokaci, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Monrovia, domin kai ziyara a kasar Sudan.

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta yi ban kwana da Hu Jintao a filin jiragen sama.

A rana daya da shugaba Hu ke ziyara a kasar Liberia, Hu Jintao ya yi shawarwari da takwararsa Ellen Johnson-Sirleaf, kuma ya gana da mataimakin shugaba kuma shugaban majalisar dattawa Joseph Nyuma Boakai da shugaban majalisar wakilai Edwin Melvin Snowe da kuma shugaban wucin gadi na majalisar dattawa Isaac Wehyee Nyenabo. Ban da wannan kuma, Hu Jintao ya halarci cibiyar shawo kan zazzabin cizon sauro ta Sin da Liberia, kuma Hu ya ziyarci Sinawa masu kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Liberia.

A ran nan a birnin Monrovia, kasashen Sin da Liberia sun bayar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa, inda aka yaba wa aminci da ke tsakanin Sin da Liberia, kuma sun yarda da kara yin mu'amala da juna da kara amincewa juna da kara hadin kai a fannoni daban daban, ta yadda za a kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu.(Danladi)