Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 09:13:13    
Shugaba Hu Jintao ya yi shawarwari da takwaransa Paul Biya na kasar Kamaru

cri

Gidan Rediyon Sin ya ruwaito mana labari cewa, a ran 31 ga watan, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Kamaru ya yi shawarwari da takwaran aikinsa na kasar Kamaru a birnin Yaounde, babban birnin kasar. Duk bangarorin biyu sun amince da yin kokari tare don ciyar da huldar abokantaka ta hadin gwiwa da sabuwar dangantakar abokantaka bisa muhimman tsare-tsare tsakaninsu gaba.

Don aiwatar da nasarorin da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, shugaba Hu ya bayar da shawararsa a kan yadda za a raya huldar abokantaka tsakanin kasashen Sin da Kamaru: Wato a karfafa amincewar siyasa da hadin gwiwa tsakanin juna; da ciyar da hadin gwiwar cinikayya bisa moriyar juna gaba; da kara musaya da hadin gwiwa tsakanin juna a fannin zamantakewar al'adu; da kuma inganta daidaitawa da tsare-tsare a fannoni dabam dabam domin ciyar da kafa wata duniya mai jituwa ta dawamammen zaman lumana da bunkasuwa tare gaba.

Yayin da ake zantawa a kan huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka, shugaba Hu ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta taba samun moriyarta ta hanyar bata moriyar sauran kasashen duniya ba. Bangaren Sin ya sa ido sosai a kan nasarorin da aka samu a taron koli na Beijing, kuma zai dukufa wajen taimaka wa kasashen Afirka ta yadda za su bunkasa cikin cin gashin kai, da kuma sanya wadannan nasarorin da aka samu su amfani jama'ar Afirka.

A wannan rana kuma, shugaba Hu ya gana da Mr. Cavaye Yegjie Djibril, shugaban majalisar dokokin kasar Kamaru, bangarorin 2 sun yi shawarwari a kan batun inganta hadin kai na kasashen nan 2.(Murtala)