Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 19:45:18    
Ziyarar da shugaba Hu Jintao zai kai wa Afirka na da muhimmanci sosai

cri
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai wa kasashe 8 na Afirka ziyara wato Cameroon da Liberia da Sudan da Zambia da Namibia da Afirka ta Kudu da Mozambique da kuma Seychelles tun daga ran 30 ga wannan wata zuwa ran 10 ga wata mai zuwa, bisa gayyatar da shugabannin wadannan kasashe 8 suka yi masa. Wannan ne karo na farko da shugaba Hu zai kai wa kasashen waje ziyara a shekarar nan, shi kuma muhimmin lamari ne daban wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Jami'an harkokin waje da masanan kula da batun Afirka na kasar Sin na ganin cewa, ziyarar da shugaba Hu zai yi ziyara ce da za a yi wa dukan kasashen Afirka don aiwatar da sakamakon taron koli na Beijing, tana da muhimmiyar ma'ana wajen inganta zumuncin gargajiya da ke tsakanin Sin da Afirka da zurfafa hadin gwiwarsu domin moriyar juna da kuma tabbatar da samun ci gaba tare.

A matsayinta na kasa mai tasowa, wadda ta fi girma a duk duniya, har kullum kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashe masu tasowa, musamman ma da kasashen Afirka. A gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a nan Beijing a karshen shekarar bara, shugaba Hu Jintao ya gabatar da matakai 8 don daukaka ci gaban hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban daban, a madadin gwamnatin Sin:'Da farko, kasar Sin za ta kara bai wa kasashen Afirka taimako, yawan taimakon da kasar Sin za ta bai wa Afirka a shekara ta 2009 zai ninka sau 1 bisa na shekara ta 2006. Na biyu, nan da shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta nuna wa kasashen Afirka fifiko wajen bayar da rancen kudi da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 3 da kuma rancen kudi da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 2 a fannin shigo da kayayyaki daga Afirka bisa gatanci. Na uku?'

Wadannan matakai 8 sun girgiza jama'ar Afirka sosai. A kwanan baya, mataimakawan ministan harkokin waje na kasar Sin Zhai Jun ya bayyana cewa,'Shugaba Hu zai kai wa Afirka ziyara ne don kara karfafa da inganta da kuma bunkasa zumuncin gargajiya da ke tsakanin Sin da Afirka. Ban da wannan kuma, za a nemi habaka hadin gwiwa don moriyar juna a tsakanin bangarorin 2. A kan hanyar ziyarar shugaba Hu, za a yi harkoki da yawa don aiwatar da wadannan matakai 8.'

Kasashen Afirka na zura ido kan ziyarar da Mr. Hu zai yi a wannan karo, haka kuma kasashen duniya na mai da hankulansu a kanta.

An yi karin haske cewa, a lokacin ziyararsa, shugaba Hu da shugabannin kasashen 8 za su yi musayar ra'ayoyinsu kan yadda za a karfafa zumuncin gargajiya da ke tsakaninsu da kuma ingiza hadin gwiwarsu daga dukan fannoni a cikin sabon halin da ake ciki, sun kuma daddale yarjejeniyoyi a jere kan hada kai ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Sa'an nan kuma, Mr. Hu zai halarci wasu harkokin da suka shafi ayyukan tallafawa Afirka ko kuma na hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

An ce, shugaba Hu zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Sudan kan batun Darfur a lokacin da yake yin ziyara a Sudan.

Madam He Wenping, mai nazarin al'amuran Afirka na cibiyar kimiyyar zaman al'ummar kasar Sin ta bayyana ra'ayinta kan dadalin da ya sa Mr. Hu zai kai wa kasar Sudan ziyara, ta ce,'Da farko kasarmu da kasar Sudan mun sada zumunci a tsakaninmu tun da can, kuma kasar Sudan ta zama ta farko wajen kulla huldar diplomasiyya a tsakaninta da Sin a cikin dukan wadannan kasashe 8, shugaba Al-Bashir ya taba kawo wa kasar Sin ziyara sau 3, amma shugabanmu zai kai wa kasarsa ziyara a karo na farko. Ko shakka babu ziyarar da za a yi a wannan karo za ta karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen 2. Ban da wannan kuma, ziyarar da shugaba Hu zai yi za ta nuna cewa, kasarmu na mai da hankali a kan yankin Darfur, a sa'i daya kuma, za mu ci gaba da taka rawa mai yakini a kan wannan batu.'(Tasallah)