Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-01 20:52:39    
Ana tafiyar da ayyukan lura da yara mata a jihar Guizhou don hana rashin daidaito tsakanin jinsin maza da mata

cri

Wannan shi ne wani ajin musamman da ke kauyen Gaozhai na gundumar Kaiyang da ke jihar Guizhou ta kasar Sin, dalilin da ya sa muka ce shi ne wani ajin musamman shi ne sabo da dukkan 'yan makaranta da ke cikin ajin su ne yara mata, wadanda suka taba yin watsi da karatu sakamakon talauci, amma yanzu sun sake shiga makaranta sakamakon taimakon da gwamnatin wurin ta bayar.

Lan Xiaoyan mai shekaru 14 da haihuwa tana daya daga cikinsu. Iyayensu manoma ne, kuma mahaifinsa nakasashe ne, shi ya sa ba ya iya yin ayyuka masu yawa. Sabo da haka har kullum su kan gamu da matsalar kudi. Yau da shekaru 4 da suka gabata, Lian Xianyan ta yi watsi da karatunta ba tare da son rai ba sakamakon talaucin da ke fama da shi.

A jihar Guizhou, yara mata da yawa sun gamu da irin wannan matsala, kuma yawan yara mata da suka rasa damar karatu ya yi matukar yawa idan an kwatanta shi da na yara maza, wannan ya shaida cewa, yara mata da maza sun sha bamba sosai wajen matsayin zamantakewar al'umma. A daidai sabo da kasancewar ra'ayin nuna fifiko ga maza bisa ga mata, shi ya sa ba a iya samun daidaito tsakanin jinsin maza da mata ba.

Sabo da haka ayyukan lura da yara mata da jihar Guizhou ta gudanar zai sa kaimi ga yin zaman daidaici tsakanin maza da mata, ta yadda za a iya hana rashin daidaito tsakanin jinsin maza da mata. A shekara ta 2003, an fara gudanar da ayyukan a duk fadin jihar Guizhou sannu a hankali. Kuma bisa taimakon da gwamnatin jihar ta bayar, an kara kafa wani aji a makarantar firamare na kyaunen Gaizhai wanda Lan Xiayan ke ciki domin daukar yara mata da suka rasa damar ci gaba da karatu. Sabo da haka, Lan Xiaoyan ta iya ci gaba da karatu. Kuma ta gaya mana cewa, "lokacin da malamai da shugaban makarantarmu suka zo gidana don gaya mini labarin kan cewa, na iya sake shiga makaranta, na ji mamaki sosai. Kuma a hakika dai na ji farin ciki kwarai da gaske, sabo da na iya ci gaba da karatu da kuma jin dadin zamana da ke cikin makarata."

Bayan shekara ta 2003, gwamnatin jihar Guizhou ta iya zuba jari fiye da yuan miliyan 2.4 don taimaka wa yara mata da su ci gaba da karatunsu. Ban da wannan kuma hukumomin da abin ya shafa sun kara ba da taimako ga mata wajen neman samun aikin yi, ta yadda za a iya sa kaimi ga yin zaman daidaici tsakanin maza da mata.

Jihar Guizhou tana kudu maso yammacin kasar Sin, yawancin mutanenta manoma ne, kuma tattalin arzikinta yana baya. Dalilin da ya sa ba a son haihuwar jarirai mata shi ne sabo da mata ba su iya yin ayyukan noma masu yawa. Sabo da haka an fara ba da taimakon kudi ga iyayen da suka haifi jarirai mata domin karfafa kwarin gwiwar manoma da su haifi jarirai mata ta hanyar ba da kudi. Bisa tsarin da aka tsara a duk kasar Sin, game da manoma da suka da da ko diya guda ko kuma suna da yara mata biyu, bayan da shekarunsu ya kai 60 da haihuwa, gwamnatin kasar Sin za ta samar da taimakon kudi ga ko wanensu yuan 600 a ko wace shekara. Kuma game da iyayen da yaronsu na farko mace ce, kuma ba su cikin shirin ci gaba da haihuwa, za a ba su kyautar kudi yuan 4000. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa shekara ta 2004, yawan kudin da gwamnatin jihar Guizhou ta zuba a wannan fannin ya zarce yuan miliyan 40.

A waje daya kuma, an aiwatar da dokokin haramta tantance jinsin jariri kafi a haife shi cikin tsanake a jihar Guizhou domin kawar da zabar jinsin jarirai da aka yi. Sabo da zab da ciki na halas ne a kasar Sin, shi ya sa wasu iyayen da suke son yara maza su kan yi amfani da na'urar zamani don tantance jinsin jariri kafin a haife shi, ta yadda za su iya zabar jinsin jariri. Domin warware wannan batu, a shekara ta 2003, gwmanatin kasar Sin ta bayar da dokoki a hukunce domin haramta tantance jinsin jariri kafi a haife shi. Zhou Chengzhou, shugaban kungiyar yin haihuwa bisa tsari ta jihar Guizhou ya bayyana cewa, "A shekara ta 2005, gwamnatin jihar ta tsara da kuma bayar da ka'idoji, inda aka haramta tantance jinsin jariri kafi a haife shi da kuma zub da ciki bisa zabar jinsi. A shekara ta 2006, mun tsara wani doka daban wajen ba da kyauta ga wadanda suka ba da rahoto kan mutanen da suka karya ka'idojin haramta tantance jinsin jariri kafi a haife shi da kuma zub da ciki bisa zabar jinsi. Wadannan dokoki da ka'idoji sun ba da muhimmin tasiri wajen ciyar da ayyukanmu gaba."

Kuma bisa labarin da muka samu, an ce, ta wadannan matakan da ake dauka, matsalar rashin daidaito tsakanin jinsin jarirai maza da mata ta jihar Guizhou ta fara samun kyautatuwa. Bisa sabuwar kididdigar da aka bayar a shekarar da muke ciki, karo na farko ne an samu rayuwa tsakanin daidaicin jinsi na jarirai maza da mata a wasu yankunan da ke jihar Guizhou. Kande Gao)