Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 16:00:28    
Mata masu ciki da ke da kiba sun fi haihuwar jarirai masu kiba

cri

A cikin kwanakin nan, manazarta na kasar Amurka sun gano cewa, idan mata masu ciki suka kamu da ciwon sakamakon kiba fiye da kima, to mai yiyuwa ne yaransu za su gaji ciwon. Sakamakon haka a cikin shekarun nan da suka gabata, yawan jarirai masu kiba na kasar Amurka ya samu karuwa sosai.

Bisa labarin da muka samu a tashar Internet ta mujallar Nature ta kasar Birtaniya, an ce, bayan da manazarta na kwalejin ilmin likita na jami'ar Harvard ta kasar Amurka suka yi bincike, sun gano cewa, muhimmin dalilin da ya sa wasu yara suke da kiba fiye da kima shi ne sabo da nauyin jikin iyayensu mata ya karu sosai yayin da suke da ciki.

Akwai dalilai da yawa da suka haifar da wannan hali da ake ciki. A wasu lokuka, idan nauyin jikin mata masu ciki ya samu karuwa fiye da kima, to za su kamu da ciwon sukari sakamakon samun ciki, sabo da haka yawan sinadarin insulin da ke jikin jariransu zai karu, wanda zai sa jarirai su kara son cin abinci, ta haka sannu a hankali nauyin jikin jarirai ya kan karu fiye da kima. Ban da wannan kuma, nauyin jikin iyaye zai taka rawa ga nauyin jikin jariransu ta maniyyi da ovum.

Haka kuma nazarin ya bayyana cewa, abinci zai ba da tasiri ga nauyin jikin jarirai. Nauyin jikin jariran da aka ciyar da su da garin madara zai karu mafi sauri idan an kwatanta shi da wadanda suka sha nonon iyaye mata.

To, yanzu za mu gabatar muku da wani bayani daban game da mata masu ciki.

Manazarta na kasar Birtaniya sun gano cewa, idan mata masu ciki suna shan magungunan ba da kafiya ga lafiya da ke kunshe da bitamin E yadda ya kamata, to za a iya rage yawan jariran da ke kamuwa da ciwon fuka sosai.

Manazarta na jami'ar Aberdeen ta kasar Birtaniya sun gano cewa, yawan jariran da suka kamu da ciwon fuka wadanda iyayensu mata ne suka shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da bitamin E kadan lokacin da suke da ciki ya ninka har sau biyar idan an kwatanta shi da wadanda iyayensu mata suka sha magungunan da ke kunshe da bitamin E da yawa. Sabo da haka kwararru sun ba da shawara cewa, ya kamata mata su sha magungunan ba da kafiya ga lafiya da ke kunshe da bitamin E yadda ya kamata lokacin da suke da ciki ba da dadewa ba.

Amma a waje daya kuma manazarta sun nuna cewa, ba wajibi ba ne mata masu ciki su sha magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da bitamin E mafi yawa, cin abinci yadda ya kamata ya isa. Bisa labarin da muka samu, an ce, abincin da ke kunshe da bitamin E da yawa su ne man girki da gyada ko makamanta da dai sauransu.

Yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani game da kungiyoyin jiyya na Red Cross da ke kauyukan kasar Sin.(Kande)