Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-10 18:53:56    
Babban dakin tunawa da marigayi Lin Zexu

cri
An haifi Li Zexu ne a shekarar 1785 a wani gidan masani a birnin Fuzhou na lardin Fujian na kasar Sin. Babansa Lin Binri wani malami ne matalauci. Amma yana da babban buri na samun ci gaba kan hanyar zaman rayuwa, yana kokari wajen aiki ba tare da tsangwama ba. Amma sakamakon kokarin bai zo masa da dadi ba, sai ya yi wa dansa Li Zexu begen alheri.

Lallai Lin Zexu bai kauce wa burin babansa ba. Tun yana yaro ya yi namijin kokari wajen karatu. Bayan ya girma, ya taba yin aiki a lardin Zhejiang ,da lardin Jiangsu, da lardin Hubei, da lardin Henan da kuma lardin Shandong da dai sauran wurare, inda ya kula da aikin siyasa da soja, da aikin samar da gishiri da na tsare ruwa, da rage harajin da aka dauka kan hatsi, da daidaita matsalar ambaliyar ruwa ta kogin Rawaya da dai makamantansu. Lin Zexu ya gudanar da harkoki bisa matsayin daidaici da kuma dokoki. Ya gwanance wajen aiki, musamman ma ya yi suna kuma ya samu karbuwa sosai daga jama'a lokacin da yake kan mukamin babban kantoman lardin Hunan da Guangdong saboda ya gudanar da harkar hana tabar Wiwi.

Ayyukan mafi muhimmanci da ya yi a lokacin da yake mulkin lardin Guangdong su ne tsayawa tsayin daka kan soke cinikin tabar Wiwi da kone irin wadannan miyagun kwayoyi a bakin teku na Humen a shekarar 1839. Ayyukan da ya yi ya sa kaimi ga dukan mutanen Sin a lokacin nan da kuma sage gwiwa ga 'yan kasashen Amurka da Birtaniya 'yan cinikin tabar Wiwi sosai.

An gina babban daki a shekarar 1905 don tunawa da babbar gudummawar marigayi Lin, an yi masa kwaskwarima da kuma canja sunansa zuwa babban dakin tunawa da Lin Zexu a shekarar 1982. Fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 3, ya nuna halin musamman na gine-gine na gargajiya na kasar Sin sosai.(Tasallah)