Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-10 18:52:59    
Dadaddun kantuna na Beijing

cri
Beijing wani birni ne mai dogon tarihi, shi ya sa ban da wasu shahararrun wuraren shakatawa, akwai dadaddun kantuna a nan, wadanda suke ci gaba da cinikinsu har zuwa yanzu. A cikin shirinmu na yau, bari mu jagorance domin kai ziyara a wasu tsoffin kantuna da tarihinsu ya kai shekaru fiye da 100, wadanda za su bayyana muku tarihin birnin Beijing da kuma labarunsa.

Kanti mai sayar da magunguna mai suna Tong Ren Tang kanti ne mafi tsufa a nan Beijing. Ko kusa wannan tsohon kanti, wanda aka bude shi a shekarar 1669, ya wakilci dadaddun kantuna na Beijing.

Wani babban jami'i mai ilmin likitanci sunansa Le Xianyang ya bude wannan kanti mai sayar da magunguna na Tong Ren Tang. Saboda ya bauta wa sarki na lokacin nan, ya yi aiki kusa da iyalan sarki, sa'an nan kuma, ya mai da hankali sosai kan albarkatun magunguna da samar da magunguna, shi ya sa kantin Tong Ren Tang ya zama kanti ne kawai da ke samar wa iyalan sarki magunguna. Mr. Jin Yongnian, wanda ya yi shekaru da yawa yake aiki cikin kantin Tong Ren Tang, ya yi karin haske cewa, kantin Tong Ren Tang ya sami takardun sayen magani da yawa daga fadar sarakuna. Ya kara da cewa, kantin Tong Ren Tang yana bin wata ka'idar samar da magunguna a tsanake, wato ko da yake ba a san yadda ake samar da magunguna ba, amma ko kusa kada masu samar da magunguna su yi sakaci. Mr. Jin ya yi bayanin cewa, kantin Tong Ren Tang ya yi shekaru fiye da 300 yana bin irin wannan al'adar gargajiya, yana mai da hankali sosai kan samar da ko wane irin magani.

Yanzu kantin Tong Ren Tang ba wani kanti mai sayar da magunguna kawai ba, har ma ya wakilci al'adar magungunan gargajiya na kasar Sin. A cikin 'yan kwanakin nan da suka wuce, an tanadi takardun sayen magani da fasahar samar da magunguna da kantin Tong Ren Tang ke mallaka cikin takardar sunayen abubuwan tarihi na al'adun gargajiya wadanda ba su kai na a-zo-a-gani ta kasar Sin ta rukuni na farko.

Idan an tabo magana kan tsofaffin kantuna na Beijing, kada a manta da shahararren kanti mai sayar da shayi mai suna Zhang Yiyuan, wanda ke da shekaru fiye da 100. Shayi mafi shahara da kantin Zhang Yiyuan ke sayarwa shi ne shayi na furen jasmine. Ruwan shayi na da tsabta, bayan a sha irin wannan shayi, sai a ji kamshi a baka, yana da matukar dandano. Shugaban kantin Zhang Yiyuan Mr. Liu Jiabo ya bayyana cewa, an fi mai da hankali kan zaben albarkatun shayi a lokacin da aka samar da shayi na furen jasmine. Ya ce,'An samar da irin wannan shayi da koren shayi da furannin jasmine. Tilas ne an yi amfani da koren shayi da aka samu a lokacin bazara. Ya fi kyau a cire furannin jasmine a lokacin zafi. Saboda idan an kara yin zafi, furannin jasmine sun kara yin kamshi. Ya kamata a cire furannin kafin su yi toho. Idan furannin sun yi toho, kamshinsu ya kare, furannin sun zama banza.'

Mutane sun iya sayen shahararrun shayi iri daban daban da aka saba sha a kasar Sin da kuma kayayyakin shayi a kantin Zhang Yiyuan. Sa'an nan kuma, idan mutane su yi gajiya, to, sun iya zauna a cikin wannan kanti, wanda cike yake da kamshin shayi, su sha shayi na furen jasmine, su saurari labarun shayi, ko kuma yi kallon wasan kwaikwayo na fasahar shayi ta gargajiya ta kasar Sin.

A karshe dai, za mu gabatar muku da kanti mai sayar da siliki mai suna Rui FU Xiang, yana daya daga cikin kantuna masu sayar da siliki mafi dadewa da suke ci gaba da bude kofarsu a nan Beijing. An bude kantin Rui Fu Xiang a karshen karnin 19. Yanzu hukumar Beijing ta mayar da shi a matsayin wurin tarihin da ake kiyaye shi.

Kantin Rui Fu Xiang na yanzu kanti ne na farko da mutane suka zaba wajen sayen siliki iri daban daban da kuma kerar tufafi iri na salon kasar Sin. An ce, an yi amfani da silikin da aka sayar a wannan kanti wajen kerar tutar Jamhuriyar Jama'ar Sin ta farko. Kantin Rui FU Xiang shi ma ya yi suna ne a ketare. An ce, matan shugabannin kasashen waje da yawa sun sayi siliki a nan a lokacin da suke ziyarar kasar Sin. Madam Setsuko Chambers, 'yar kasar Amurka, ta gaya wa wakilinmu cewa, ta ji sunan kantin Rui Fu Xiang a lokacin da take kasar Amurka. Ta ce,'Da can na san wannan kanti a cikin littattafai, an ce, silikin da ake sayarwa a nan sun sha bamban da wadanda ake sayarwa a sauran kantuna, shi ya sa na zo nan sayen siliki. Na sayi wasu abubuwan musamman ga mutanen kasar Amurka. Na yi zumudi sosai.'(Tasallah)