Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-23 15:07:19    
Kasar Iran ta ba da amsa a rubuce kan shirin kuduri na kasashe 6, kasashen duniya sun mai da martani kan wannan

cri
Ran 22 ga wata a Tehran, Ali Larijani, babban wakilin shawarwarin nukiliya na kasar Iran ya gana da jakadun kasashen Rasha, da Sin, da Ingila, da Faransa, da Jamus da ke kasar Iran, da kuma jakadan kasar Swiss da ke Iran bisa matsayinsa na wakilin kasar Amurka, kuma ya ba da amsa a rubuce kan shirin kudurin da kasashe 6 suka yi dangane da warware matsalar nukiliya ta Iran.

Yanzu, ba a sanar da hakikanin abubuwan da ke kunshe a cikin amsar da Iran ta bayar ba. A wannan rana Mr. Larijani ya bayyana cewa, kasar Iran tana fatan ba da taimakonta a kokarin da ake yi na warware matsalar nukiliya bisa matsayinta na wata kasar da ke iya dauki nauyi. Kasar Iran ta riga ta shirya sosai, domin yin tattaunawa da kasashe 6 daga ran 23 ga wata.

Ran 23 ga wata, ofishin kakaki na ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu bangaren Sin yana nazari sosai kan amsar da Iran ta bayar. Kullum bangaren Sin yana ganin cewa, warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, wannan ne hanyar da ta fi kyau, kuma ta dace da moriyar bangarori daban daban.

A ran 22 ga wata, John R. Bolton, wakilin din din din na kasar Amurka da ke M.D.D. ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta yi nazari kan amsar da Iran ta bayar, idan amsar ba ta iya biyan bukatun kasashe 6, kasar Amurka za ta sanya takunkumi wajen tattalin arziki ga kasar Iran ta kwamitin sulhu na M.D.D. a farkon wata mai zuwa. (Bilkisu)